Uncategorized

Yan Bindiga Sun aika Wanda Yaƙi Aurar Da Diyarshi Ga Mai Gidansu A Zamfara har lahira

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe wani mutum a kauyen Kwalfada da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara saboda ya ki aurar da ‘yarsa ga abokin aikinsu.

A cewar wani mazaunin unguwar, Usman Magaji, daya daga cikin ‘yan fashin ya nemi auren daya daga cikin ‘yan matan kauyen amma mahaifin yarinyar ya ki amincewa da hakan.

Yan Bindiga Sun aika Wanda Yaƙi Aurar Da Diyarshi Ga Mai Gidansu A Zamfara har lahira
Yan Bindiga Sun aika Wanda Yaƙi Aurar Da Diyarshi Ga Mai Gidansu A Zamfara har lahira

Magaji ya bayyana cewa mahaifin yarinyar ya yanke shawarar aurar da ita ga wani dan kauyen, inda ya yi watsi da bukatar barayin, jaridar liberty tvr na ruwaito a shafin na sada zumunta.

Bayan an daura auren, sai ‘yan fashin suka far wa kauyen inda suka kashe mahaifin yarinyar.

’Yan ta’addan sun kuma bukaci sabon mijin da ya yi aure ya gaggauta sakin matarsa domin abokin aikinsu ya aure ta.

Sun yi barazanar kashe mijin idan bai bi umarnin da suka gindaya masa na sakin matarshi ba.

Nan da nan sai mijin ya saki matar kuma ta sake aure ga dan fashin da ya kai ta daji inji shi.

Magaji ya kara da cewa ‘yan fashin sun dade suna ta’azzara wa al’umma saboda rashin samar da tsaro ga al’umma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button