Tiriliyan Ɗaya N1.57 Baza Ta Wadatar Wajen Yaƙi Da Matsalar tsaro A Najeriya ba. Ministan Tsaro Ya Buƙaci a ƙara Kasafin kuɗin Ma’aikatarsa.


Ministan tsaron Najeriya, Badaru Abubakar, ya miƙa kokon bararsa ga Majalisar dokokin kasar, inda ya roke su da su kara wa ma’aikatarsa kasafin kudin shekarar 2024.
Ya yi ikirarin cewa kudin da ake ware na Naira tiriliyan 1.57 a Yanzu bai isa ba. Yadda ya kamata wajen Yakar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.


Badaru ya Gabatar da nasa ra’ayin ne a Jiya Laraba yayin wani zama da kwamitin tsaro na majalisar dokokin kasar. Ya bayyana cewar tashin farashin man fetur da kuma tsadar man dizal, yasa aka samu Gagarumin ci gaba a kasafin kudin ma’aikatar.jaridar liberty Tvr na ruwaito.
Ya kuma kara jaddada matsalolin kudi da hauhawar farashin kaya da kuma tsadar man fetur ke haifarwa. Ya kuma yi tsokaci na musamman kan yawan man fetur da dizal da rundunonin soji ke amfani da su a fadin kasar nan.
Duk da karancin kudi, Badaru ya tabbatar wa kwamitin cewa duk kudaden da aka ware za a yi amfani da su ta hanyar da ta dace. Ya jaddada gaskiya da rikon amana, inda ya ce:
“Za mu bibiyi wannan kashe-kashen da kuma tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware za a yi amfani da su sosai, Kuma za mu yi lissafin yadda ya kamata.”
Duk da haka, Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan Harƙar Tsaro, Ahmad Lawan, ya nuna shakkunsa. Ya jaddada buƙatar a samu kwararan hujjoji na yadda za’a ƙara kasafin Kuɗin ma’aikatar.