Labarai

Shi Talakan Najeriya Tamkar Ragon Daji Yake -Shaikh Zakzaky

Advertisment

Shi Talakan Nijeriya tamkar Ragon Daji ne, yace idan mafarauci na so ya kama Ragon daji, to zai haƙa masa tarko ne, idan Ragon ya kamu mafarucin zai tafi ne ya bar Ragon cikin Tarkon, ba zai dawo wurin ba sai ya tabbatar da cewa yunwa ta fara galaɓaitar da shi.

Ya ce, idan mafaraucin zai koma duba ragon, zai riƙe abinci a hannu, ta yadda da zarar Ragon ya ga abincin zai fara rawar jiki, alamun yana buƙatar abincin, shi kuma mafaraucin zai riƙa wurga masa abincin kaɗa-kaɗan. Ya ce a haka zai riƙa yi masa yana ba shi abinci kafin ya cire shi a cikin Tarkon, har sai Ragon ya ji cewa wannan mutumin masoyinsa ne, tunda yana kawo masa abinci, alhali kuwa shi ne wanda ya ɗana masa tarkon da ya kama shi.

Shi Talakan Najeriya Tamkar Ragon Daji Yake -Shaikh Zakzaky
Shi Talakan Najeriya Tamkar Ragon Daji Yake -Shaikh Zakzaky

Mafaraucin ba zai cire shi daga Tarkon ba, har sai ya ga sun shaƙu da ragon, ko da ya je kusa da shi bazai cutar da shi ba, sannan zai cireshi daga Tarkon.

Shaikh Zakzaky ya ce to haka Talakan Nijeriya yake, da zarar sun ga masu Mulki, za ka ga suna rawar jiki, suna cewa ‘Ranka ya daɗe’!!!, Sai a ɗan wurga musu wani abu, alhali kuwa su ne suka talautar da mutane.

Advertisment
Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button