Labarai

Shehu Sani ga gwamnoni: Ku dena ɗiban kuɗin talakawa ku na kai wa Tinubu gaisuwa a jiragen haya

Advertisment

Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi kira ga gwamnonin Najeriya da su daina barnatar da kudaden jama’a wajen ɗaukar jiragen haya domin kai gaisuwa ga shugaba Bola Tinubu.

Ya kuma roki shugaban kasar da ya hana gwamnoni barin jihohinsu a lokutan bukukuwa saboda kalubalen tsaro da ake fuskanta.

Jaridar liberty tvr na ruwaito cewa Sani wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani a kan ziyarar da kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, ‘su ka kaiwa Tinubu a gidansa da ke Legas a jiya Talata, ya koka da cewa hakan na da illa ga tattalin arziki da tsaro ga gwamnatocin jihohi.

Shehu Sani ga gwamnoni: Ku dena ɗiban kuɗin talakawa ku na kai wa Tinubu gaisuwa a jiragen haya
Shehu Sani ga gwamnoni: Ku dena ɗiban kuɗin talakawa ku na kai wa Tinubu gaisuwa a jiragen haya

A wani sako da ya wallafa a sashihin shafin sa na X a jiya Talata, Sani ya ce irin wadannan ziyarce-ziyarcen na kara wa jihohi nauyi mai yawa na kudi, yana mai jaddada cewa ya kamata shugabannin Najeriya su yi da gaske wajen rage kudin gudanar da mulki.

“Bayan wadannan bukukuwan, ya kamata shugaban kasa ya hana gwamnonin jihohi barin jihohinsu don kai masa gaisuwa.

“Na farko, babban nauyi ne a kan kudaden jihohi. Farashin jirage masu haya da sauran kuɗaɗe.

“Na biyu kuma, da alama ana samun ci gaba da fuskantar barazanar tsaro a lokutan bukukuwan.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button