Labarai

Sanatocin Nijeriya sun sadaukar da albashinsu na watan Disamba ga mutanen kauyen Tudun Biri

Sanatoci 109 na Nijeriya sun ba da kyautar albashinsu na watan Disamba ga iyalan da bam ya shafa a kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna

Sanatocin sun sanar da hakan a ranar Lahadi, lokacin da suka kai ziyarar ta’aziyya da jajanta wa ga iyalai da gwamnatin jihar Kaduna.

Sanata Barau Jibrin da ya jagoranci tawagar ya ce kudin da suka ba da gudunmuwa sun kai Naira milyan 109.

Wani labari:Dole a kamo waɗanda suka saki bom kan masu mauludi a kaduna – sheikh Bauchi

Ba zamu lamunta ba, dole a kamo waɗanda suka saki bom kan masu mauludi a jihar Kaduna, kuma a hukunta su

Babban Malamin addinin Musulunci A Najeriya Maulanmu Shaikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira na gaggawa ga hukuma kan Kisan masu Mauludi yace gwamnati ta daina wasa ana kashe rayukan mutane yace lallai wannan karon baza su bari ba, dole ne gwamnati ta fito ta kama duk wani mai hannu a kisan ta gurfanar da shi a yanke masa babba hukunci daidai da abinda ya aikata.

Shehin Malamin cikin wani faifan bidiyo da babban dansa Alhaji Ibrahim ya fitar ya Kara da cewa haka shekarun baya ma jama’arsu sun fito Zikirin Juma’a aka taresu aka yanka su, gashi yanzu ma an jefawa wasu Bom Dan haka baza su bari ba-Inji Shehin MalaminMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button