Rarara Yana Kira Ga Al’ummar Jihar Kano Da Su Yi Murna Cikin Nutsuwa
Fitaccen mawakin Siyasa a nahiyar Afrika, Dauda Kahutu Rarara ya yi kira ga Al’ummar Jihar Kano, da za su fito murna a lokacin da za a bayyana nasarar karshe ta Gawuna/Garo da su fito cikin natsuwa ba tare da tada hankalin kowa ba,shafin zinariya tv na ruwaito a shafinsu na sada zumunta.
A cewarsa, babu abin da su ke so irin ci gaban Jihar Kano, don haka za su fito murna bayan yanke hukuncin karshe, amma ba za su fito don tada hankalin kowa ba, ko kuma don kona dukiyar kowa ba, ko yin wata hayaniya da za ta sanya Al’umma dar-dar ba.
Rarara ya bayyana haka ne a wani gaggarumin taro da ya shirya a jiya Litinin, 11 ga watan Disamba 2023 dakin taro na Otal din Bristol da ke Kano.
Sannan ya yi wa masoyansa albishir da sabuwar wakar sa da zai saki mai taken 4-0.
Wani labari: Rarara ya sake zunguro sama da kara a wata sabuwar hirarsa
Gidan rediyo rfi hausa sun samu tattaunawa da dauda kahutu rarara akan kalamansa da na tayar da kura a kafaffen sada zumunta na arewacin najeriya akan gwamnatin ta da shude da caccakar tsohon shugaban kasa muhammadu buhari.
Mutane wasu suna Allah wadai da irin butulcinsa wasu kuma suna nuna cewa ae wannan dabi’a ce ta makori kamar karuwa ne, amma mawaka basa son ana kiransu da wannan kalma ana alakanta su da kare,ga yadda zantawar ta kasance tsakanin rarara da rfi hausa.