AddiniLabarai

Musabaƙa 2023 : Bauchi da kano sune sunka Lashe Gasar Karatun Alkur’ani na ƙasa na 38

Advertisment

Malama Zainab Aliyu Muhammad daga Jihar Kano ta zama Gwarzuwar Gasar Alkur’ani ta Kasa ta shekarar 2023 a bangaren mata a hadda da tafsiri.

A bangaren maza kuwa, Alaramma Ibrahim Muhammad Nasir daga Jihar Bauchi ne ya zama Gwarzon Shekara a musabakar karo na 38, wadda aka kammala a Jihar Yobe.

Mai Masaukin Baki, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karamma Malama Zainab Aliyu Muhammad daga Jihar Kano da kyautar mota kirar Honda Accord.

Musabaƙa 2023 : Bauchi da kano sune sunka Lashe Gasar Karatun Alkur'ani na ƙasa na 38
Kyautar malama zainab kenan ta naira miliyan 5

Jaridar Aminiya na ruwaito,Alaramma Ibrahim Muhammad Nasir kuma gwamnan ya gwangwaje shi da kyautar mota kirar Honda Accord.

Advertisment

Sannan ya ba da kyautar bas mai daukar mutum 18 kirar Toyota Hummer ga Kwamitin shiryar musabaka na Kasa don ci gaba da dawainiyar gasar Alku’rani.

Musabaƙa 2023 : Bauchi da kano sune sunka Lashe Gasar Karatun Alkur'ani na ƙasa na 38
Kyautar Naira Miliyan 5 ta Alaramma Ibrahim Muhammad Nasir

A ranar Asabar din nan aka kammala Gasar Karatun Alkur’anin ta Kasa karo na 38 a Damaturu, fadar Jihar Yobe inda alarammomi daga sassan Najeriya suka nuna bajintarsu.

A lokacin rufe gasar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yaba wa matasan da suka shiga wannan gasar ta Karatun Alkur’ani Mai Girma rukuni-rukuni, sannan ya yi musu fatan alheri.

Musabaƙa 2023 : Bauchi da kano sune sunka Lashe Gasar Karatun Alkur'ani na ƙasa na 38
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Kenan tare da Gwani Alammara

Sarkin Musulmi, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya nuna farin cikinsa bisa yadda aka gudanar da gasar a Yobe cikin kwanciyar hankali kuma a bisa tsari ba tare da an samu cikas ba.

Musabaƙa 2023 : Bauchi da kano sune sunka Lashe Gasar Karatun Alkur'ani na ƙasa na 38
Malama Zainab Aliyu Muhammad daga Jihar Kano

Shi ma Shugaban Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Lawan Sulaiman Bilbis ya yaba wa gwamna Mai Mala Buni bisa yadda ya dauki nauyin gasar da kuma yadda aka gudanar da ita cikin nasara.

Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Danfodiyo ne dai ke shirya Gasar Alkur’ani ta Kasa a Najeriya, kuma wanan shi ne karo na 38.

Musabaƙa 2023 : Bauchi da kano sune sunka Lashe Gasar Karatun Alkur'ani na ƙasa na 38
Alaramma Ibrahim Muhammad Nasir daga jihar bauchi

Mahalarta bikin rufe gasar ta Alkur’ani sun hada da Gwamna Jihar Gombe, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, Mataimakin Gwamna Jihar Borno, Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba.

Sai masu girma sarakunan Jihar Yobe gaba daya, karkashin Mai Martaba Sarkin Fika, sai Mai Martaba Shehun Dikwa da ya wakilci Mai girma Shehun Borno, sai Mai girma Sarkin Bauchi da sauran manya-manyan baki.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button