Matsalar tsaro : Mutane na tserewa daga Kidandan a Kaduna
Daruruwan jama’a na ci gaba da tserewa daga garin Kidandan da ke karamar hukumar Giwa a jihar kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, sakamakon ƙaruwar hare-haren da ‘yan bindiga da ke ci gaba da kai wa garin.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce maharan sun addabi garin na Kidandan inda suke kashe mutane tare da garkuwa da wasu domin neman kudin fansa baya ga tsawwala wa jama’a musamman manoma biyan haraji.
Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa, sai da suka shafe kwanaki shida kullum sai ‚yan bindiga sun shiga garin.
Ya ce,“ Kullum mutanen nan sai sun shigo sun yi harbe-harbe, su dauki mutane su tafi, muna kwana cikin zaman dar dar, wallahi yanzu halin da muke ciki a Kidandan muna cikin yanayi na damuwa.“
Mutumin ya ce,“ A yanzu magidanta da yara musamman mata, idan ka ga yadda mata da yara ke tafiya abin sai ya baka tausayi basu san inda za suje ba saboda tashin hankali.“
Ya ce, suna kwana cikin firgici, amma duk da haka jami’an tsaro na kawo musu dauki, domin suna musayar wuta da su, sai dai bayan sun tafi sai kuma su dawo.
Mazaunin garin ya ce, suna bukatar gwamnatin tarayya da ta jiha su taimake su domin yadda ‘yan bindiga suka addabe su.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa, ba Kidandan kadai ake kai harin ba, har da kauyukan da ke makwabtaka da shi.
Ya ce,“ Yadda mazauna Kidandan ke barin garin haka su ma na kauyukan ke fita, saboda suna ganin babu dalilin da zai sa su zauna alhali a kullum sai an kai hari garin da suke karkashinsa.“
Garin Kidandan dai ya shafe tsawon watanni yana fama da hare haren ‘yan bindiga‚ waɗanda galibin lokuta kan dorawa mutane harajin da ya fi karfinsu musamman manoma.
Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro musamman na hare haren ‘yan bindiga wadanda ke satar mutane don kudin fansa wani lokaci ma har da kisa.
Duk da kokarin da gwamnatin tarayyar Najeriyar ke cewa tana yi da ma gwamnatin jihar Kaduna ta Kaduna don kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi yankunan arewacin kasar, har yanzu ba ta sauya zani ba.