

Shafin jibwis Nigeria sun wallafa wata gagaru da walimar yaya dalibar da sunka haddata Alkur’ani mai girma wadda ya samu halarta manya manyan malamai na Nigeria da wajen Nijeriya.
Makarantar Haddar Al’quran mai suna “Tsangayar Sheikh Abdullahi Bala Lau” ta yaye dalibai sama da 30 wadanda suka haddace Al’qurani mai girma a garin jalingo.
Taron na Yaye dalibai Mahaddata Alkur’ani Wanda Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Waikamatis Sunnah (Jibwis Nigeria) Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya assasa a jahar Adamawa, Taraba, Jigawa da FCT tana yaye dalibai a ko wace shekara na mahaddata al’qurani mai girma.
Shugaban Majalisar Malamai Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Sheikh Dr. Kabiru Haruna Gombe, Alaramma Ahmad Suleiman Kano da Alaramma Nasiru Salihu Gwandu da sauran jama’a suka samu Halartan taron a dakin taro na Muslim Council dake Jalingo a jahar Taraba
Kazalika an karama Shugaban da lambar yabo na Kadimul Kur’an, sheikh Bala Lau ya dauki dawainiyar karatun yara biyu daga cikin mahaddan har zuwa inda hali yayi.