Labarai

Labarin yaro mai baiwar tsince-tsince a Kano, mahaifinsa ya kai matarsa da mahaifinta

Advertisment

Kamar Al’mara, Wata shari‘a na gani a kotun shariar musulunci dake karkashin Ustaz Ibrahim Sarki Yola.wani mutum ne ya Kai karar matar sa da mahaifin ta, dan jarida nasiru salisu zango ne ya wallafa labarin a shafin na sada zumunta.

Yake shaidawa kotu cewar, suna da dan su mai shekara 11 kuma tun yaron yana shekara 9 aka gano yana da wata baiwa domin yana yawan tsinto abubuwa masu daraja, misali ko hannun sa ya saka cikin kwatami sai kaga ya tsinto Zinare haka yake kaiwa gida a sayar ayi bushasha.
Wata rana suna tsince tsince da abokan sa kawai sai ya tsinto wata jaka cike da daloli yaro ya dauka ya kaiwa mahaifiyar sa,ita kuma nan take ta kira mahaifin ta sannan kuma ta kira mijin ta.

Labarin yaro mai baiwar tsince-tsince a Kano, mahaifinsa ya kai matarsa  da mahaifinta
Labarin yaro mai baiwar tsince-tsince a Kano, mahaifinsa ya kai matarsa da mahaifinta

Can sai mahaifin ta Malam Ya‘u ya fara zuwa ta bashi labari kuma ta dauki sunki 50 na dalar (wrapper 50) ta bashi ya tafi.

Bayan ya tafi ne sai kuma ga mijin ta Bashir yazo inda shikuma ta bashi labarin dalolin da Idrisa ya tsinto amma fa, ta gaba masa cewar, ta baiwa mahaifin ta bandir 50 abin da ya Rage a yanzu bandir biyar amma Zata ajiye a hannun ta bayan shekara guda Idan mai su bai bayyana Ba sai a kasafta.

Advertisment

Dole a Haka mijin nata ya amince, amma bayan shekara da wannan batu bayan da ya lura Ana ta facaka sai ya Bukaci a fito da kudi, nan matar ta shiga yi masa hanya hanya daga nan ya kira mahaifin ta Dan Jin inda aka kwana shikuma mahaifin nata yake shaida masa cewar Ai dama wannan kudi da yake tunanin daloli ne takardu ne Dan haka babu wannan maganar ta dala.

Wannan shine ya fusata Bashir ya garzaya kotu yayi kara.

Koda yake Lauyan wadanda aka yi Kara bai amsa Da’awar Ba amma alkali yayi tambaya shin da aka tsinci kudin an yi cigiya? Aka ce masa a a ba‘ayi cigiya Ba an dai ajiye ne ko mai su zai yi cigiya

A karshe mai sharia ya dage shariar,kuma ya sanya a ranar zama na gaba azo masa da yaron domin zai yi masa tambayoyi Shi da Shi.

Shin wai wannan baiwar tsince tsince ta yaron nan baiwa ce daga Allah ko gamo yayi da sarikul jinnu?

Yanzu ya za su yi idan sanadiyar wannan shari’a mai kudin ya bayyana?

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button