Labarai

Kotu Ta Daure Mutum Biyu Kan Laifin Lalata Da Kananan Yara

Babbar kotun jihar Jigawa dake zamanta a Birnin Kudu karkashin mai shari’a Dr. Musa Ubale, ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan wani mutum mai suna Isa Manga.

Wanda ake tuhumar mai shekaru 45 dan asalin garin Kiyako dake cikin karamar hukumar Birnin Kudu.

Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan samun sa da laifin yin lalata da wasu kananan yara mata su biyu a cikin wani gina da ba a kammala ba.

A wani labarin mai kama da wannan, babbar kotun ta zartar da hukuncin daurin rai dai a gidan kurkuku kan wani matashi mai shkekaru 25 mai suna Israfilu Sagiru.

Matashin dan asalin garin Zarena dake cikin karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa, an yanke masa wannan hukuncin ne bisa samun sa da laifin yin lalata da wasu Almajirai biyu.

Mai shari’a Musa Ubale na babbar kotun jihar Jigawa dake Birnin Kudu, yace wannan hukuncin zai zama izina ga sauran masu kokarin aikata irin wannan laifi.

Kotun ta zartar da wannan hukuncin ne bisa tanadin dokar jihar Jigawa mai lamba 3 (2) da kuma doka ta 4 kan cin zarafin jama’a.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button