KISAN TUDUN BIRI: Iyalan wadanda suka rasu sun maka gwamnatin Najeriya da rundunar Sojoji a Kotu, suna bukatar a biya su diyyar naira biliyan 33


Iyalan wadanda suka rasu a harin Tudun Biri da yayi sanadiyyar sama da mutum 86 a kauyen tudun Biri dake jihar Kaduna, sun maka gwamnatin tarayya da sojojin Najeriya a kotu, suna bukatar a biya su diyyar naira biliyan 33 diyyar rayukan ;yan uwansu da suka rasa.
Tun bayan aukuwar hatsarin gwamnatin tarayya, da rundunar sojin Najeriya suka amsa laifi inda mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima, da shugaban rundunar sojin Najeriya Taoreed Lagbaja suka kawo ziyayrar musamman kauyen Tudun Biri.
Mai shigar da kara, Dalhatu Salihu, a karar da aka shigar a ranar 8 ga watan Disamba, amma PREMIUM TIMES ta gani a ranar Talata, ya ce ana tauye wa mutanen da aka kasshe hakki rayuwa da suke da shi ta hanyar kashe su ta dalilin wannan harida suka hada da wani Sani Sulaiman, Salima Abdurrahman, Ibrahim Idris,ni da wasu 50.


Ya nemi a biya diyyar rayukan wadanda aka kashe wanda basu ji ba basu gani, har naira biliyan 33. A baiwa iyalan mamatan a matsayin diyyar rayukan ‘yan uwansu da aka kashe.
mai shigar da kara ya ce a kudin da suke nema a biya na diyyar rayukan wadanda aka kashe ne a wannan rana.
” Ko da muka ji saukar bam din sai na arce da gudu. Wasun mu da ke tsakiyar wannan wuri sun rasu. bincike na farko da muka bayan lafawar lamarin mun tara gawarwaki har 93 a lokaci daya..
PREMIUM TIMES ta gano har yanzu ba a mika shari’ar ga kowani alkali ba domin a afar sauraren karar.