Labarai

Kasafin kuɗin da Tinubu ya gabatar cike yake da bashi da yaudara

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana kasafin kuɗin ƙasar 2024 a matsayin “na yaudara wanda ba shi da wata takamaimiyar manufa ta gayaran tattalin arziki”.

A ranar Laraba ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin kuɗi na 2024 ga taron haɗin gwiwa na ‘yan majalisar tarayya.
Kasafin da Tinubu ya yi wa laƙabi da “kasafin sabunta fata”, an gina shi kan hasashen farashin gangar ɗanyen mai dala 96, kuma gwamnati na fatan samar da gangar danyen mai miliyan ɗaya da dubu 78 a kowace rana, yayin da musayar dala ɗaya za ta kasance kan naira 750.

A jawabinsa, Tinubu ya ce kasafin zai mayar da hankali kan abubuwa uku; tabbatar da tsaro, ƙirƙirar ayyukan yi, da kuma rage talauci.

Kasafin kuɗin da Tinubu ya gabatar cike yake da bashi da yaudara
Kasafin kuɗin da Tinubu ya gabatar cike yake da bashi da yaudara

“[Wannan kasafi] babbar cuta ce wadda idan aka ƙyale ta wuce za ta ƙara shaƙe wuyan ‘yan Najeriya kuma ta jefa ƙasar cikin ƙangin tattalin arziki da rashin tabbas,” in ji PDP cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta PDP ta mayar da hankali takamaimai kan yawan kuɗin da za a kashe wajen biyan bashi na naira tiriliyan 8.25 da kuma wagegen giɓi na naira tiriliyan 18 da za a cike shi ta hanyar cin bashi da kuma ƙara yawan harajin da ake karɓa.

“A bayyane take cewa kasafin mai cike da tanadin jin daɗi ga fadar shugaban ƙasa da shugabannin jam’iyyar APC, an tsara samo kuɗin ne ta hanyar ciyo bashi da kuma ƙara wa ‘yan Najeriya haraji, wanda hakan zai ƙara jefa ƙasa cikin bashi da kuma ƙuntata wa ‘yan Najeriya da ke cikin ƙangi.”

Cikin kundin da gwamnatin ta miƙa wa majalisa, an tanadi kashe naira tiriliyan 9.92 a matsayin kuɗin ayyukan yau da kullum, da kuma tiriliyan 8.7 a matsayin na manyan ayyuka.
Wannan ne cikakken kasafin kuɗi na farko da Tinubu ya gabatar tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a watan Mayun da ya wuce bayan ya karɓi mulki a hannun Muhammadu Buhari na jam’iyyarus ta APC.

Ba kamar yadda aka saba ba, har shugaban ya kammala jawabinsa bai bayyana adadin kuɗaɗen da aka ware wa ma’aikatu da hukumomin gwamnati ba.
Ya nemi majalisun tarayyar, ta wakilai da ta dattijai, da su tsefe tare da amincewa da kasafin cikin kwana 30.

Mu mun gaji da ciyo bashi – LP

Tinubu ya gabatar da kasafin ne ga taron haɗin gwiwa na ‘yan majalisar wakilai da dattawa
Gwamnatin APC ta ce tana tsammanin tattalin arzikin ƙasa zai haɓaka da aƙalla kashi 76 cikin 100, fiye da abin da aka yi hasashe.
Haka nan, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta daidaita hauhawar farashi a kan kashi 21.4 cikin 100 a 2024, saɓanin 27.33 da aka samu a watan Oktoba da ya gabata.
Sai dai, ba jam’iyyar PDP ce kawai ta soki tanade-tanaden kasafin kuɗin ba. Ita jam’iyyar adawa ta Labour Party ta ce ita ma ba ta ga inda gwamnatin APC za ta samo kuɗin biyan bashin da take ciyowa ba.

“Mu mun gaji da cin bashi. Jam’iyyar LP na cewa a nemi kalar bashin da za a tallafa wa ƙasa, saboda a yanzu ba masana’antu ake taimaka wa ba waɗanda za su kawo kuɗin shiga,” kamar yadda Yunusa Tanko, mai magana da yawun kamfe ɗin ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, ya bayyana.
“Idan da za su iya yin haka to ƙila su kamo bakin zaren. Amma yanzu motoci kawai suke saya don su hau, da kuma neman sayen jirgin ruwan ba mu buƙatar sa.”
Bashi ba alheri ba ne ga kowace ƙasa – Ɗan majalisa

Ya zuwa watan Satumban 2023, bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 87.38.
Wannan kasafi ya tanadi biyan bashin naira tiriliyan 8.25 a 2024 – kashi 45 cikin 100 ke nan na jimillar abin da Najeriya za ta samu daga abubuwan da take samarwa a cikin gida.
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Muhammad Bello Shehu, ya ce akwai matsaloli game da ciyo bashi.
“Bashin nan ba a naira za a ciyo shi ba, a dala za a karɓo shi.

To ita dalar yaya take yanzu a ƙasar?
Muna ma da dalar a ajiye a asusunmu na ajiya a ƙasashen waje?”
Da aka tambaye shi idan ba a ciyo bashin ba ta yaya za a iya aiwatar da kasafin?
“Sai mu yi kasafi daidai da aljihunmu. Kamar yanzu da aka gina kasafin kan gangar mai miliyan 1.78 duk rana, shin akwai zaman lafiyar da za a iya haƙo wannan man a yankunan da ake da shi?”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button