Labarai

Kano: Ƴansanda sun kama mutane 9 bisa zargin sayar da yara ƙanana

Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta kama wasu gungun masu safarar ƙananan yara da suka kwarw wajen sata da saye da siyar da ƙananan yara.

Da ya ke gabatar da wadanda ake zargin s gaban ƴan jarida a shelkwatar rundunar a yau Alhamis, Kwamishinan Ƴansandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel ya ce an kamo su ne sakamakon bayan sirri.

Kano: Ƴansanda sun kama mutane 9 bisa zargin sayar da yara ƙanana
Kano: Ƴansanda sun kama mutane 9 bisa zargin sayar da yara ƙanana

Daily Nigerian hausa ta ruwaito,ya ce mutanen tara da aka kama suna aikata wannan mummunan laifi ne a jihohin Kano, Bauchi, Lagos, Delta, Anambra da Imo.

Gumel ya ce an ceto yara bakwai daga hannun waɗanda ake zargin.

A cewar Gumel, a ranar 15 ga Disamba, da misalin ƙarfe 3:25 na yamma, jami’an rundunar a yayin sintiri na sirri, su ka cafke wata mai suna Comfort Amos, mai shekara 45 da ke zaune a Tudun Wada, yayin da ta ke shirin safarar wani yaro zuwa Legas, mai suna Abdulmutalib Sa’ad, dan shekara 5 da ke Unguwar Zango a jihar Bauchi.

Ya kara da cewa binciken da akai musu ya sanya aka kamo wata mai suna Chika Ezugbu, mai shekara 52, mazauniyar Sabon Gari, Joy Nzelu, itama mazauniyar Sabon Gari, Clement Ali, dan shekara 35 dake Badawa da kuma Emeka Ekeidigwe, shima a Sabon Gari, dukkansu a jihar Kano.

Ya ce bincike ya nuna cewa sun sayar da yaran a garuruwa da dama kan wasu kudade da suka kai N480,000 dubu N450,000 da sauransu.

Ya ce rundunar xs ta ci gaba da kokarin an kuɓutar da irin wadannan yara, inda ta ce tuni iyayen su sun zo kuma sun gan su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button