Labarai

Ka gayawa Tinubu gaskiyar halin da Najeriya ke ciki – Fayemi ga Ganduje

Advertisment

Wani tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Kayode Fayemi, ya bukaci shugaban jam’kyyar APC, Umar Ganduje, ya sanar da shugaba Bola Tinubu game da hakikanin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki.

Fayemi ya ce kamata ya yi Ganduje ya bai wa Tinubu ra’ayi daga al’umma don kada shugaban kasa ya dogara da abin da yake ji a “Villa da ya kulle.”

Tsohon gwamnan ya yi magana ne a ranar Talata a wajen wani tarom ƙaddamar da littafi mai suna: ‘APC & Transition Politics’, wanda wani jigo a jam’iyyar APC, Salihu Lukman ya rubuta.

Ka gayawa Tinubu gaskiyar halin da Najeriya ke ciki – Fayemi ga Ganduje
Ka gayawa Tinubu gaskiyar halin da Najeriya ke ciki – Fayemi ga Ganduje

Ya kuma bukaci jam’iyya mai mulki da ta cika takardar ta kuma kada ta zama ‘yar kallo’ wajen tsara manufofi.

Advertisment

Tsohon gwamnan ya koka da yadda mawakan yabo suka sa wadanda ke fadar shugaban kasa ke da wuya su san hakikanin halin da ‘yan Najeriya ke ciki.

A cewar Fayemi: “Na yi farin ciki da shugabanmu ya zo nan. Wannan ita ce jam’iyyar da bai kamata ta zama ‘yar kallo ba wajen tsara manufofi.

“Ya kamata wannan jam’iyya ta zama ita ce za ta tsara tsarin jam’iyyar.

“Ya kamata wannan jam’iyyar ta kasance ita ce ta gaya wa shugaban kasa cewa wannan ra’ayi ne daga al’umma da mazabu da ke can, ba wai abin da yake ji a Villa da aka kulle shi ba.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button