Labarai

Gwamnatin Sakkwato za ta sayi motocin Naira biliyan 1.1 ga ofishin gwamna

Advertisment

A jiya Laraba ne gwamnatin jihar Sokoto ta amince da sayen motocin da kudinsu ya kai Naira biliyan 1.1 ga ofishin gwamnan.

Amincewar wani bangare ne na wasu kwangilolin da aka bayar kan kudi Naira biliyan 19.

Jaridar daily Nigerian hausa na ruwaito,Kwamishinan yada labarai na jihar, Bello Danchadi, ya shaidawa manema labarai a Sokoto a karshen taron mako-mako na majalisar zartarwa ta jihar cewa, kwangilolin na cikin alkawuran yakin neman zabe da gwamnan ya yi.

Ya ce majalisar ta kuma amince da gina titunan cikin gari guda 47 a unguwar Tudun Wada da Unguwar Rogo a cikin babban birnin Sokoto kan kudi naira biliyan 8.9.

Ya ce an kuma bayar da kwangilar gine-gine da gyaran hanyoyin gari a yankin Runjin Sambo kan kudi Naira biliyan 2.1 da na Titin Bidinga a kan Naira miliyan 816.2.

Kwamishinan ya kara da cewa sauran kwangilolin da aka bayar sun hada da sake gina titin Lodge da Force Avenue, Kalambaina, Roul-Mairuwa, da Tsohuwar Kasuwa a kan kudi kimanin naira miliyan 800.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button