Gwamnati za ta biya diyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin bam da sojoji suka kai Tudun Biri’
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta biya diyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sanadin harin bam da jirgi sama maras matuki na rundunar sojin kasa ya kai a garin Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Mataimakin shugaban kasar Kashin Shettima ya sanar da haka yayin wata ziyara daya kai Kaduna a baya baya nan.
Ya ce za’a gina makarantu da asibiti da kuma gidaje don inganta rayuwar al’ummar dake zaune a yankin.
Sanata Kashim Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya da ta kai ziyara Kaduna da ta kunshi kakakin majalisar wakilai da ministan tsaro na kasar.
Gwamnan jihar Kadunan Sanata Uba Sani ya shaida wa BBC cewa mataimakin shugaban kasan ya bayyana haka ne a lokacin da suka ziyarci wadanda su ka samu raunuka da suke samun kullawa a asibitin gwamnati na Barau Dikko:.
“Mataimkain shugaban kasa da shugaban kasa sun tattauna kuma an dauki mataki yanzu, wadanda suka hada da gina wa wadanda a’lamarin ya rutsa da su gidaje sannan kuma za a gina mu su asibiti da makaranta kuma za a taimaka mu su da harkar noma”, in ji hi
Gwamna ya kuma bayyana cewa shugaba Bola Ahmad Tinubu ya amince da kiran da ya yi a kan cewa ya kamata a biya wadanda al’amarin ya rutsa da su diyya:
“Z aa tattauna da shugabbanin adini domin a fidda adadin hakkin nasu saboda an yi taro da shugabbanin adinin musulunci da kuma na kirista saboda akwai mutun uku wadanda ba musulmi ba da suka rasa rayukansu a harin”, in ji shi.
Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki dawainiyyar wadanda suka jikkata da ke karbar magani a asibiti kuma akwai tanadin da ta yi wa yara da suka rasa iyayansu kamar yadda gwamna Uba Sani ya bayyana:
“Zamu tabbatar da cewa wadanda suka rasa iyayensu watau marayu , gwamnatin jihar Kaduna ta dauki nauyinsu, duk da cewa ita ma gwamnatin tarayya za ta biyasu hakkinsu “, in ji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasa ya bada tabbacin cewa za a gudanar da bincike kan a’lamarin kuma gwamnati jihar Kaduna za bi sahu
Fatan gwamnatin jihar Kdaun ashi ne kada a sake samun aukuwar al’amari irin wannan.