Gwamnan Kano ya kaddamar da fara biyan ƴan fansho sama da 5,000 haƙƙunan su


A yau ne Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da fara biyan ƴan fansho sama da dubu biyar haƙƙunan na bayan ritaya daga aiki.
Gwamnan ya ce gwamnatin sa ta ware Naira biliyan 6 domin biyan kudaden giratuti da na ma’aikatan da suka rasu.
Da ya ke jawabi a bikin kaddamar War, wanda ya gudana a yau Asabar a gidan gwamnatin Kano, Gwamna Abba ya ce ya cika alkawarin da ya dauka tun lokacin da ya ke yakin neman zabe.
A cewar sa, gwamnatin ta baiwa ƴan fansho da ma’aikata muhimmanci, inda ya ce da zuwan su, sun gaji makudan bashi har na Naira biliyan 48.6 da ƴan fansho ke bin gwamnati.
Gwamnan Ya kuma ci alwashin cewa zai ci gaba da biyan kuɗaɗen giratuti har sai ya biya bashin da gwamnatin baya ta tara nan da watanni 20 masu zuwa.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa shugabannin ƙwadago da na yan tanshin duk sun yabawa gwamnan bisa wannan bakinta da suka ce ba a taba samun irin ta a tarihin Kano ba.