Labarai

Gara wanda ya rasu yana zina,luwaɗi da wanda ya rasu wajen mauludi – sheikh baffa hotoro

Bayan kai harin bam din da sojojin Nigeriya sunkayi wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama, wanda kowa sai dai ya fadi albarkancin bakinsa cewa mutum dari ne, mutum dari da wani abu ne da dai sauransu.

Shine mutane suke kyautatawa wadanda bayin Allah zato cewa sunyi shahada tunda sun mutu wajen taron bukin murna zagayowar mutuwar fiyayyen halitta annabi muhammad (s.a.w).

To shine sheikh baffa hotoro matashin malami dan jihar kano dake arewacin Nijeriya yake cewa sam babu wannan magana cewa sunyi shahada ga abinda yake cewa akan wani faifan bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta.

Gara wanda ya rasu yana zina,luwaɗi da wanda ya rasu wajen mauludi
Gara wanda ya rasu yana zina,luwaɗi da wanda ya rasu wajen mauludi

“Muguwar cikawa ina zancen wani shahada ina zancen shahada ana maganar muguwar cikawa, abinda yafi zina da yan luwadi da sunka mutu suna luwadi gara su da wanda ya mutu yana mauludi maganar gaskiya kenan, waɗannan sun mutu suna bidi’a wadanda sun mutu suna saɓon Allah.

Ina fatan ana fahimta, ina magana ita bidi’a inda munninta yake wanda duk wanda yake saɓon Allah yana nufin manzon Allah (s.a.w) bai isar da musuluncin nan dai dai ba, kuma bai isar da shi a cike ba- inji Baffa hotoro.

Ga bidiyon nan.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button