Labarai

Farfesa Ali pantami ya baiwa Hafizai Mahaddata Alkur’ani Kyautar danƙararen motoci

Advertisment

Farfesa Ali isah pantami ya ji dadi sosai ziyarar da gwanayen hafizai mahaddata Alkur’ani mai girma sun ka kai shi ziyarar inda ya wallafa a shafinsa na jin dadin wannan ziyarar da sunkayi masa kamar haka.

“Professor Isa Ali Pantami ,CON da Gwarzon Shekara da Gwarzuwar Shekara na musabaqar Qur’ani na shekara 2022. Sun ziyarci Professor Pantami tare da yan’uwansu da malamansu da abokanensu.
Allah Ya sa Qur’an ya cecemu gobe Kiyama.”

Shine malam farfesa Ali isah pantami ya gwangwaje musu kyautar danƙararen motoci ga wannan hafizai wanda tabbas sunci wannan kyauta domin irin hazakar da sunkayi, muna rokon Allah yasa Alkur’ani ya cecemu gobe alkiyama amen.

Farfesa Ali pantami ya baiwa Hafizai Mahaddata Alkur'ani Kyautar danƙararen motoci
Farfesa Ali Pantami da Nura Abdullahi Bello Guiwa (MODIBBON SOKOTO)

Shafin modibbon Sokoto sun wallafa godiya da wadannan zaratan mahaddata Alkur’ani sunkayi inda sunka mika godiyar su ga babban shehin malamin Farfesa Ali Isah Pantami kamar haka.

SAQON GODIYA

Assalamu Alaikum wa Rahmatullah.

A Madadin Ni Nura Abdullahi Bello Guiwa (MODIBBON SOKOTO) da Kuma Gwarzuwa Aisha Abdulmutallib Yobe Muna Mika Cikakkiyar Godiyar Mu ga Professor Isa Ali pantami akan Gagarumar Karramawa Da Yayi Mana da Kuma Kyautar Motoci da Yabamu Kirar ‘Corolla LE’ biyo Bayan Samun Nasara Da Muka yi a Musabaqar qasa Shekarar da ta Shude. Allah ya Saka Masa da alkhairi ya biya da Gidan Aljanna.

Farfesa Ali pantami ya baiwa Hafizai Mahaddata Alkur'ani Kyautar danƙararen motoci
Farfesa Ali Isah Pantami Da Aisha Abdulmutallib

Zanyi Amfani da wannan Dama inyi Kira ga Shuwagabannin mu akan Suyi Koyi da Professor Wurin qarfafa Duk Wanda Ya taka Wata Rawar Gani a Kowane Irin Fanni na karatun Addini Domin Zaburar Wa Ga Sauran Masu Tasowa.

Har Wa Yau Zanso in yi Kira da Jan Hankali ga Yan uwa da ake Cikin Gwagwarmaya Iri daya akan Cewa Wadannan Kyautuka Girman Su Bai Kai ace Niyyar Mu ta karkata Zuwa Yi Don Su ba. Asalin kyauta da Girmamawa Suna RANAR GOBE.

Allah yasa Muyi Saboda Shi Ya qara Mana albarka a Rayuwar Mu.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button