Labarai

Dantsamage ya zazzaga ƙwallaye 5 yayin da Pillars ta yiwa Gombe United  5-2

Dan wasan gefe na Kano Pillars, Yusuf Abdullahi wanda aka fi sani da Ɗantsamage, a yau Lahadi ya zura kwallaye biyar rigis a ragar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Gombe United a gasar Firimiya ta Najeriya, NPFL.

Wasan shine na mako na 11 na gasar NPFL 2023/2024, wanda aka buga a filin wasa na Pantami Township dake Gombe, inda Pillars ta lallasa Gombe United da ci 5-2, yayin da Abdullahi dan shekara 18 ya ci dukkan kwallaye biyar ɗin.

Daily Nigerian hausa na ruwaito da yake zanta wa da manema labarai bayan kammala wasa, Abdullahi Maikaba, kocin Kano Pillars, ya bayyana farin ciki matuƙa ga sakamakon wasan.

Maikaba ya ce ya yi matukar farin ciki da yadda daya daga cikin matasan ‘yan wasansa a kungiyar ya ci dukkanin kwallaye biyar bayan da ya ke ta fama da don ya fara cin ƙwallaye a wasannin da suka gabata.

“Abin farin cikina shi ne, daya daga cikin hazikan ‘yan wasan da ke tasowa a Najeriya ya zura kwallaye biyar. Rana ce mai ban al’ajabi ga Kano Pillars, ni da tawaga ta,” inji shi.

Da yake yabawa Abdullahi, Maikaba ya ce dan wasan ya yi ta yunkurin jefa kwallo ta farko ga kungiyar amma sai yau ya samu dama.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button