Daga yanzu duk kamfanin da zai dauki Fim sai ya sanar da mu – Abba Al-Mustapha
Hukumar ta ce Fina-finai ta jihar Kano, ta ce, duk kamfanin da zai yi aikin ɗaukar shirin Film, sai ya sanar da ita, sakamakon gyare-gyaren da hukumar ta zo da shi don tsaftace harkar a tsakanin al’umma.
Shugaban hukumar Abba Al-Mustafa ne ya bayyyana hakan a safiyar wannan rana ta cikin shirin barka da hantsi, na Freedom Radio Kano, ya ce ɗaukar matakin ya zama wajibi don gudun abin da ka je ya zo.


“Akwai bukatar al’umma da sauran hukumomin Gwamnatin tarayya dana jiha su ba mu hadin kai don ganin mun cimma burin mu na tsaftace harkar fina finan na Hausa; yadda za mu yi dai-dai da addini da al-adun Hausawa, “in ji Al-Mustapha”.
Wani Labari : Kuskure ne mutum ya siyar da Kodarsa saboda matsin rayuwa – Ma’aikacin Lafiya
Kwararren ma’aikacin lafiya dake Asibitin kwararru na Murtala Muhammad a jihar Kano, Ali Ibrahim Tofa, ya ce kuskure ne mutum ya siyar da Kodarsa, don za’a bashi kudi saboda matsin rayuwa da yake fama da shi.
Ali Tofa ya bayyyana hakan ne ga gidan rediyon Dala FM, biyo bayan matakin da gwamnatin tarayya ta ce za ta dauka a kan likitoci da mutanen dake da hannu wajan safarar kodar mutane zuwa kasashen waje.
Ya ce abun takaicin ma shi ne yadda ake amfani da takaicin mutane a ba su abun da bai taka kara ya kaeya ba, da zummar an sai kodar ta su.