Labarai

Bayan sace sarki da fadawa 22, sun sungumi mai Shari’a a taraba

Advertisment

Yayin da al’ummar Jihar Taraba ke zaman zullumi da jimamin takaicin yadda ‘yan bindiga suka arce da wani basaraken jihar da fadawan sa 22, sai kuma ga shi wasu ‘yan bindiga sun arce da mai shari’a, sun yi garkuwa da ita, bayan sun bindige dogarin ɗan sandan da ke tsaron lafiyar ta.

Mai Shari’a a Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom, Justice Uwana ta faɗa hannun ‘yan bindiga waɗanda suka arce da ita ranar Litinin, kan hanyar ƙaramar hukumar Oron.
Haka nan kuma, a ƙoƙarin arcewa da ita sai da suka bindige ɗan sanda mai tsaron lafiyar ta har lahira.

Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom, Odiko MacDon ya tabbatar da labarin yin garkuwa da babban mai shari’ar.
Ya ce Mai Ta haɗu da ‘yan bindiga lokacin da ta ke kan hanyar komawa Uyo, babban birnin jihar, bayan ta tashi daga zaman kotu a garin Oron.

Yan bindiga sun sace sarki da fadawa 22, sun sungumi mai Shari'a a taraba
Bayan sace sarki da fadawa 22, sun sungumi mai Shari’a a taraba

Haka nan kuma PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda a baya-bayan nan wasu ‘yan bindiga suka sauke lodin makaɗa, mawaƙi, ‘yan rawa, ‘yan amshi da sanƙira, suka nausa da su cikin dokar daji.

Fitaccen mawaƙin ‘balaja’u’, rawar kwambilon da aka fi sani da kiɗan juju, Omoba De Jombo, ya faɗa hannun ‘yan bindiga, shi da ɗaukacin tawagar sa kakaf.

Sauran waɗanda aka yi garkuwar tare da shi, sun haɗa da dukkan tawagar da suka haɗa da ‘yan rawa, ‘yan amshi har ma da sanƙira.

An kama su ne kan hanyar su ta zuwa Kogi daga Abuja domin zuwa raƙƙashewa a Jihar Kogi.

Waɗanda suka yi garkuwa da su dai sun ce ba za su sake su ba sai an biya diyyar Naira miliyan 10 kan kowane mutum ɗaya.

Wani mawaƙi ne mai suna Adeyinka Adeboye ya fara watsa labarin yin garkuwa da tawagar ɗan uwan sa mawaƙin a shafin sa na Instagram, lamarin da ya ja hankulan jama’a da dama.

Boyebest ya ce masu garkuwar sun bugo waya, sun nemi a biya diyyar Naira miliyan 10 kan kowane mutum ɗaya.

Abokan sana’ar sa dai na ci gaba da muna damuwa da kuma addu’ar neman kuɓutar su.

Ya ce an kama su ne kan hanyar su bayan sun dawo daga Jihar Ondo, inda suka je suka yi wasa.

Wani mai suna Aysneakey ya bayyana cewa cikin waɗanda aka yi garkuwar da su, akwai ɗan’uwan sa ɗaya.

Ya ce an kama su ne tsakanin titin Obajana/Kabba.

Sai dai kuma ba a bayyana yawan waɗanda aka yi garkuwar da su ba. Kuma ba a bayyana jinsin ‘yan bindigar da suka arce da su ba.

Haka kuma har zuwa yanzu ba a san shin har da kayan kiɗan aka haɗa aka nausa cikin daji da su ba, ko kuma a cikin mota aka bar kayan kiɗan.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button