Aure be hana boko: Uwargida Ta Lashe Lambar Yabo 23, Ta Zama Jarumar Shekarar 2023 A Karatun Likitanci A Jami’ar Danfodiyo
Wata uwargida ‘yar shekara 24, Sumayyah Abdallah ta zama jarimar dalibar fannin likitanci ta shekarar 2022/2023 kuma ta samu lambar yabo 23 a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato (UDUS).
Bugu da kari, Sumayyah ta samu kyautar kudi a bikin kaddamar da daliban likitanci da aka gudanar a dakin taro na jami’ar a ranar Asabar, 09 ga watan Disamba, 2023. Ta bayyana cewa, su kimanin 140 ne suka fara wannan zangon karatun a shekarar 2015 amma 79 ne kawai suka samu kammalawa a wannan shekarar, jaridar leadershiphausa na ruwaito.
Sumayya ta fito ne daga karamar hukumar Agaie ta jihar Neja, ta fara karatun likitanci ne a watan Disambar 2015 wanda ya kai kimanin shekaru takwas zuwa yanzun (Disamba 2023). Baya ga karramawar da aka yi mata na samun lambar yabo, Sumayyah ta samu fiye da naira N400,000 yayin kaddamar da su.
Dakta Sumayyah tayi aure a shekarar 2021 yayin da take mataki zango na 4 sannan kuma ta haihu saura sati 3 a fara jarrabawar mataki zuwa zango na 5. “Aure ne ya kara min kaimi da azama fiye da yadda nake kafin aure. na kara maida hankali sosai wajen cimma burina,” in ji Sumayyah.