An kama mijin da ya yi yunkuri tura matarsa barzahu don ya samu ƙarin harin shagonsa


Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta sanar da kama wani magidanci mai shekaru 35 da haihuwa da ake zargi da yunkuri hallaka matarsa da tabarya.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce mutumin ya sanar da su cewa ya yi yunkurin aikata hakan ne don ya samu damar sayar da talabijin dinta don ya kara jarin kasuwanci a shagonsa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ahmad Wakili.
‘Yan sandan dai sun ce mijin ya yi kuruwar cewa barayi sun shiga gidansa, ya ruga ya shiga dakin matarsa ya sanar da ita ta gaggauta rufe fuskarta. Daga nan ya fita, shi ma ya rufe fuskarsa, ya dawo cikin dakin da tabarya, ya fara jibga ma matar tabarya.
‘Yan sanda suka ce wanda ake zargin ya amsa laifin cewa ya yi niyyar kashe matar ne don ya samu damar sayar da talabijin da suke kallo a gidan, ya samu kudin da zai kara jarin kasuwanci a shagonsa.
Wani labari: An ƙaddamar da Manhajar kawo Rahoton rashawa a jihar Kano
Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, ta ƙaddamar da Manhaja mai suna “Shawarata” wacce al’ummar jihar zasu iya shigar da Rahoto akan wata rashawa ko kuma bada shawara.
Hukumar karɓar korafe-korafen al’umma da yaƙi da rashawa ta jihar Kano, karkashin jagorancin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ce ta ƙaddamar da Manhajar a safiyar ranar Asabar, yayin taron bikin ranar yaƙi da rashawa ta Duniya da aka gudanar a dakin taro na Coronation dake fadar Gidan gwamnatin Kano.
Wakilinmu Abubakar Lecturer ya rawaito cewa, gwamnan Kano wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, yace an kirkiri Manhajar ne domin tabbatar da yin Gwamnati a bude, ta yadda al’umma zasu kawo rahoton wata rashawa da su ka gani domin a dauki mataki.