Abokinsa Da Matarsa sunka hallaka shi har lahira
Wani matashi Nafiu Hafeez Gorondo dan asalin jihar Bauchi mazauni a garin kano Allah ya karbi rayuwarsa ta dalilin ana zargin abokinsa da matarsa sunka hallaka shi har lahira subhanillahi.
Majiyarmu ta samu wannan labari daga majiya mai karfi ga wani dan uwansa ya da wallafa a shafinsa na sada zumunta mai suna sunusi Dahiru gorongo inda yake cewa:
“Ɗan uwana ne na jini kuma ƙani yake a gare ni.
Ya gamu da ajalin sa ne a jihar Kano karamar hukumar Tarauni cikin unguwa uku.
Abokin sa da matar abokin nasa, su suka shirya komai da kan su, kuma matar ta amsa yi masa kisan gilla..!
Matar ta amsa da bakin ta ita ta caccakka masa wuka a wuya da kahon zuciya da kuma gefen cikin sa har ya mutu..!
Yanzu haka mutum uku suna hannun jami’an tsaro mijin da matar da kuma wanda ya tattare shi ya sa lifafa da sunan ya masa wanka
Hoton yana da daga hankali.”