Ƴan Nijeriya za su iya ɗaukar bidiyon jami’an mu a bakin aiki — Ƴansanda
Hukumar yansandan ta ƙasa ta ce ƴan ƙasar na da damar ɗaukar bidiyo da hotunan ƴansanda a lokacin da suke bakin aiki.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ƙasar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X ranar Alhamis.
Adejobi na mayar da martani ne kan saƙon da wani mai amfani da shafin ya wallafa da ya ce ‘yan sanda sun tatse shi naira 10,000 saboda bidiyon da ya ɗauke su a lokaci da suke binciken ababen hawa.
Jaridar BBC Hausa na ruwaito.Kakakin rundunar ya ce ba laifi ba ne ɗaukar hoto da bidiyon ‘yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.
Ya ƙara da cewa rundunar ta sha gaya wa mutanen cewa babu laifi ɗaukar bidiyo da hotunan ‘yan sandan da ke bakin aikin.
Mista Adejobi ya ce duk wanda ‘yan sanda suka ci zarafinsa saboda ɗaukarsu bidiyo ko hoto su kai rahoto ga hukumar ‘yan sanda.