Labarai

Ƙwallon guragu: Kano Pillars ta lallasa Sakkwato 14-1

Kungiyar kwallon guragu ta Kano Pillars, a jiya Lahadi ta yi wa takwararta jihar ta Sakkwato dakan sakwarar Legas da ci 14 da 1, inda ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Para-Sports da ake yi a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, an buga wasan ne a filin wasa na Moshood Abiola na kasa da ke Abuja.

Ana sa ran kammala wasannin da aka fara ranar Asabar, a ranar 12 ga watan Disamba.

Jaridar daily Nigerian hausa na ruwaito, tawagar ta Kano Pillars ta nuna karsashi inda suka yi amfani da kura-kuran da ‘yan wasan Sokoto suka yi wajen zura kwallaye cikin gaggawa.

Ƙwallon guragu: Kano Pillars ta lallasa Sakkwato 14-1
Ƙwallon guragu: Kano Pillars ta lallasa Sakkwato 14-1

Mubarak Ibrahim ne ya zura kwallaye hudu, Umar Dahiru ya ci shida, Ibrahim Hashim ya zura kwallaye biyu.

Sani Gimbiya da Auwalu Shuaibiu da ya sauya sheka ne suka ci wa Pillars kwallo daya kowannensu a wasan da suka tashi 14-1 da kungiyar Sokoto yayin da Lawali Mohammed ya ci wa tawagar Sokoto kwallo daya tilo.

Da yake jawabi bayan kammala wasan, Ibrahim Musa, kocin Kano Pillars Para Soccer ya ce yana da kwarin gwiwar lashe kofin.

“Wasan mu na gaba shine karfe 4:30 na yamma da kungiyar Legas kuma zan doke su da irin yawan ƙwallayen da na doke kungiyar Sokoto.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button