Kannywood

Zan kaiwa gwamna Abba Gida Gida ‘ya’yana ya cigaba da kula dasu – Malam Ali

Dakataccen jarumi a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Abdul Sahir (Malam Ali), ya ce an dakatar dashi daga masana’antar ba bisa ƙa’ida ba, saboda haka ne yayi kira ga gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, akan cewa zai kawo masa jikokinsa domin ya cigaba da kula dasu.

Cikin wani fefen bidiyo da ya wallafa a ranar Talata, Malam Ali ya bayyana gwamnan Kano a matsayin Uba a gare shi, don haka yake so ya miƙa masa ‘ya’yansa kasancewar an dakatar dashi daga sana’ar da yake kula dasu.

A ranar Litinin ne hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta dakatar dashi tsawon shekaru biyu, bisa zarginsa da wallafa bidiyon da yake furta kalaman batsa, kuma ya ƙi amsa gayyatar da akayi masa domin kare kansa.

“wannan sako ne zuwa ga mai girma gwamna Engr Abba kabir Yusuf (abba gida gida) babu wani mahaluki mai hankali yake so yaga yarsa, matarsa,kanwarsa ko antynsa tana rawar zubar da mutumci a kafafen sada zumunta suna sanya matsatsun kaya a kafaffen sada zumunta musamman kafa ta tiktok.

Zan kaiwa gwamna Abba Gida Gida 'ya'yana ya cigaba da kula dasu - Malam Ali
Zan kaiwa gwamna Abba Gida Gida ‘ya’yana ya cigaba da kula dasu – Malam Ali Hoto/Sahirabdul/Instagram

“Ya mai girma gwamna jihar kano shiyasa nake amfani da dama wajen na jawo hankalin matasan mu, da ni kai na , musamman ya’ya mata da anka sansu yakana alkunya da kamun kai.

Ya mai girma gwamna jihar kano ina tura sakonina ba tare da ba tare da cin mutumci ga addini na ko kuma jihar kano ba, ya mai girma gwamnan jihar kano a matsayin ka na uba kuma shugaba a jihar kano ina son in sanar da kai cewa an dakatar dani a Masana’atar Kannywood har tsawon shekaru biyu ba bisa ka’ida ba, an yanke hukuncin ne bidiyo bayan wani faifan bidiyo da na saki akan jawo hankalin matasa musamman ‘ya’ya mata domin su kama kansu”-inj malam ali kwana casa’inMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button