Labarai

Zan gina makarantun a jihar kogi da babu irin su a fadin duniya – Dino

Dan takarar gwamnan Kogi na APC Dino Melaye, ya bayyana cewa idan ya zama gwamna zai gina Otel Otel a saman ruwa a jihar.

” Zan gina manyan Otel a bisa ruwa idan na zama gwamna, domin in jayo masu saka jari daga kasashen waje zuwa jihar.

Babba jaridar dillanncin labarai premium times na ruwaito,bayan haka sanata Dino ya ce zai gina makarantu na zamani da babu irin su a fadin duniyan nan.

Zan gina makarantun a jihar kogi da babu irin su a fadin duniya - Dino
Zan gina makarantun a jihar kogi da babu irin su a fadin duniya – Dino

“Idan kuka zabe ni zan gina makarantu a jihar Kogi da babu irinsu a fadin duniyar nan. Za mu yi zurfin tunani akan al’amuran mu kuma ina tabbatar muku da cewa ba sa ku yi da na sanin zabe na gwamnan jihar Kogi ba.

Sannan kuma ya ce duk ma’aikatan gwamnati da gwamna Yahaya ya kora zai dawo da su aiki.

” Ina muku alkawarin cewa duk wanda gwamna Yahaya ya kora aiki, zan dawo da shi kan aikin sa.

A karshe Dino ya ce idan ya zama gwamnan kogi, zai maida madafun iko kaf dinsa ga kananan hukumomi.

” Kudaden kanana hukumomi, za a rika basu abinsu kaf dinsa. Ba za acire wa kowa komai ba daga jiha. Zan tabbata an maido wa kananan hukumomi damar kashe kudaden su domin talakawan, ba babakere da ake musu yanzu ba a jihohi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button