Zan biya duk bashin da ake bin Aminu s bono – Aisha Humaira


Fitacciyar jaruma nan makusanciya ga mawakin siyasar nijeriya Aisha Humaira ta fitar da sanarwa zata biya bashin duk wanda yake bin margayi darakta aminu s bono bashi.
Aisha Humaira ta fitar da wannan sanarwa ta faifan bidiyo tun jiya bayan sanar da mutuwarsa inda ta fadi yadda za’a tuntubeta domin kayi bayanin kowa kake binsa da yadda za’a turamaka kuɗinka.


“Tabbas mutumin kirkiri ne Aminu s bono aminina yana sona sosai domin yakan bani shawara akan duk abinda zai shafeni na aiki ko kama mancin haka zai fadi shawara sosai.
Aninu s bono na dade da shi tsawon rayuwa amma ko sa’insa bata tabamu da shi ba, to irin soyayya da kauna da ya nunamin naga babu abinda ya ragemin sai nayi masa addu’a da kuma fatan yiwa mutane rokon dan Allah duk wanda yayiwa ba daidai ba ya yafi masa.
Game da bashi kuma domin insha Allah duk wanda yake biyarsa bashi in bai fi karfina ba zan biya masa, idan kuma ya fi karfina zan nema masa taimako.
Zan saka numbobin mutane biyu da suke makusanta aminu s bono domin duk wanda yake binsa bashi sai ya kira yayi bayyani.
+234 806 084 0990 Hamza Dogo
0803 888 1014 G Boy”