Labarai

yan bindiga sun ƙone mace mai shayarwa da ƴarta a jihar Sakkwato

Mutane da dama sun rasu a wani rikicin daukar fansa bayan harin da ’yan bindiga a yankunan Karamar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato

Mutane da dama sun rasu a wani rikici da ya barke tsakanin al’ummomi bayan harin da ’yan bindiga suka kai a yankunan Karamar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato.

Majiyarmu ta ruwaito daga Aminiya ta gano ’yan bindiga sun kai hare-hare sau hudu a wasu al’ummomin yankin daga ranar Lahadi zuwa Laraba, inda suka kashe mutane da dama, ciki har da wata mai shayarwa da ’yarta da aka kona su a cikin wata motar haya.

yan bindiga sun ƙone mace mai shayarwa da ƴarta a jihar Sakkwato
yan bindiga sun ƙone mace mai shayarwa da ƴarta a jihar Sakkwato

Yan bindigar sun kuma jikkata mutane da dama suka kuma sace wasu da ba bayyana adadinsu ba, ciki har da kananan yara da matan aure.

Wani mazaunin garin Tangaza, ya shaiwa wa wakilinmu cewa bayan kammala jana’izar mai shayarwar da ’yarta ne wasu matasa da ’yan banga suka far wa kauyukan Fulani, suka kashe mutane da dama suka cinna wa gidaje wuta.

Yankunan da ’yan bindigar suka kai wa hari sun hada da hanyar Ruwan Wuri inda suka harbe wani direban motar haya suka kona motarsa da mutanen ciki da kuma Gidan Kakale inda suka sace mutane biyar.

A kauyen Alela Sutti kuma ’yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure da ’ya’yansu sannan suka je kauyen Alkasu suka sace mutum 17.

Wani mazaunin karamar hukumar Tangaza ya yi zargin cewa yawanin masu kawo harin ba ’yan Najeriya ba ne, kuma ya danganta yawaitar hare-haren ’yan bindiga a yankin da kusancinsa da dazukan Tsauna da Kuyan wadanda suka dangana da Jamhuriyar Nijar.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani kan lamarin daga kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, amma jami’in ya ce nan gaba zai yi bayani idan ya samu cikakken rahoton abin da ke faruwa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button