Wani Malami Ya Sayi Otel Ya Maida Shi Makarantar Islamiyya


Wannan shi ne Malam Nura Murtala Zawiyya, Gusau, babban Malami ne da ya shahara a jihar Zamfara. Shi ya sayi daya daga cikin manyan hotel na birnin Gausa da ya yi suna a baya, Bliss Hotel kuma ya maida shi makarantar Islamiyya.
Tuni dai aka sanya wa makarantar suna: “Madrasatu Hizburrahim Talamizatu Shaikh Ibrahim Inyass”
Bayanai sun nuna cewa, a baya wannan otel na daga cikin wuraren da ake zuwa aikata fasadi a Gusau, wanda wannan na daga cikin dalilinsa na sayan wannan wuri domin maida shi wurin da zai amfani al’umma da addinin musulunci.
Wani labari : Hukumar CCB za ta gurfanar da Muhyi Magaji Rimin Gado
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta Code of Conduct Bureau, ta sanar cewa ta kammala dukkanin shirye-shirye na gurfanar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da aka fi sani da ‘Anti Corruption’ a gabanta.
Hukumar kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ta sanar cewa a ranar Alhamis ta makon gobe 16 ga Nuwamba ne hukumar za ta gurfanar da Barr Muhyi.
Wata majiya daga hukumar ta ce za a gurfanar da Barr Muhyi ne bisa zargin wasu laifuka na gaza mika mata rubutaccen bayani game da kadarorin da ya mallaka da sauran laifuka.
A wani sammace da Magatakardan hukumar ya aike wa shugaban hukumar, an umurce shi da ya bayyana a gabanta domin amsa wasu tuhume-tuhume guda 10.