Kannywood

Waɗanda suka fi kowa shahara da kuɗi a fim, sune suka fi yaɗa ɓarna -Abdallah Amdaz

Kamar yadda hukumar hisbah tayi kira ga jaruman kannywood da masu shiryawa furodusa da kuma masu bada umurni darakta zuwa wajen hisbah domin zama da su a tattaunawa akan operation kauda badala .

Satin da ya wuce sunyi zama da yan tiktok inda sunka bada hadin kai sunka je wanda sun bada goyon bayan dari bisa dari to a yau Litinin anyi zama da yan fim suma kamar yadda sanarwa ta fita.

Waɗanda suka fi kowa shahara da kuɗi a fim, sune suka fi yaɗa ɓarna -Abdallah Amdaz
Waɗanda suka fi kowa shahara da kuɗi a fim, sune suka fi yaɗa ɓarna -Abdallah Amdaz Hoto/aamdaz/Instagram

Inda wasu jaruman kannywood ko muce shuwagabanni sunka nuna irin wannan kira da ankayi musu bai dace ba saboda su kamfanin ne da su, babu wanda ya isa ya kira su ya zauna da su akan titi.

Abdullahi amdaz daya daga cikin jaruman kannywood inda ya bayyana cewa:

Da yawan waɗanda suke samun cigaba a harkar film, su ne waɗanda suka fi zubar da mutuncinsu, sannan mafi wayan marasa abun hannu sune waɗanda suke riƙe mutuncinsu.”

Mawaƙi kuma jarumi a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Abdallah Amdaz, ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wata ganawa ta musamman da hukumar Hisbah ta jihar Kano.

Nasara Radio ta wallafa rubutun inda mutane shi kyau sharhi akan wannan maganar sa.

@Abba muazu ga abinda yake cewa:

Kafadi maganar gaskiya kuma hakane sai kaga mace tashigo fim bata shekara daya kaganta da mota shikuwa namiji sai ya shekara uku ko abun hawa babu to a ina sukesamu su matan.

@khamis k. Ahmad abinda yake cewa :

Wannan haka yake, inban mantaba itin makamancin zancen yataba, fitowa ta bakin Kabiru na Kwango, ayi film sai kaji wani Babba a kasa ya kira yarinya yabata kyauta sbd film din datayi, bayan kuma duk sune suka isar da sakon wa’azantarwa ko fadakarwa ga al’umma, amma baruwan kowa dasu.

@Dan hajiya A Yakasai cewa yake :

Ita gaskiya dai guda Daya che tal

Excellency namu.

Mujtaba magaji Goran dutse cewa yake:

Gaskiya kafada shine kokarin da Hisbah ta ke yi domin kawo sauyi a lamarin amma wasu marasa kishi suke korafi akan hukumar ta Hisbah dan haka kiran damu keyi ga hukumar Hisbah duk wani actor,producer kokuma director da bai halarci wannan gayyata ba da a gaggauta garkame ofishin sa tare da kwace lasisinsa.

Allah yakareka daga fadawa chikin tarkon makiyaMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button