Tsokaci a kan Hukuncin kotun daukaka kara a kan Zaɓen Kano- Bulama Bukarti


Barista Audu Bulama Bukarti babban lauyan nan na duniya wanda yake dan nijeriya amma mazauni Ingila ya tsokaci akan hukuncin daukaka ƙara ta abuja da tayi akan zaben gwamna jihar Kano wanda anka fafata tsakanin mai girma gwamna Engr Abba kabir Yusuf (abba gida gida) da kuma Dr.nasiru Yusuf gawuna.
Bulama Bukarti mutum ne da yake sharhi akan shari’orin nijeriya da kum harka tsaro tun daga boko haram har zuwa yanzu inda yayi fice sosai, a yau munzo muku da tsokaci da yayi na hukuncin daukaka kara da tayi appeal court kenan wanda takardun ƙara sunka jawo tayar da jijiyoyin wuya.
Mutane sunyi kira da barista yayi tsokaci akan rubutaccen hukuncin kotun daukaka kara kuma ya aminta ya dace yace wani abu, musamman akan wasu abubuwa hudu da ya shafi wannan hukunci.
Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Laraba, inda yace kotun ɗaukaka ƙarar ba zata iya gyara tufka da warwarar da tayi ba, sai dai idan anje kotun ƙoli.
“Tunda na ke a bangaren Shari’a, ban taba gani ko jin hukuncin da akayi tufka da warwara kamar na zaɓen gwamnan Kano na kotun ɗaukaka ƙara ba.”
Ga bidiyon nan ku saurara.