Labarai

Tiktoker: Kira na karuwa da malamin makarantar yayi ya ɓatamin rai sosai – Rahama Sa’idu

Rahama Sa’idu wadda anka kora a kwalejin koyon aikin jinya da ke birnin kebbi inda ta bada labarin cewa hukumar makarantar ta kore ta ne ta dalilin wai saboda tana soshiyal midiya wanda kuma hakan bai hana ta karatu ba.

Inda ta nuna cutar ta ankayi amma kuma daga baya hukumar makaranta ta karya wannan magana inda sunka nuna cewa faduwa jarabawa tayi tare da kuma rashin zuwa asibiti bada kwa kwaran dalili ba shima wannan kawai ya isa a kori dalibi daga makaranta to ita duk biyun ta hada kamar yadda hukumar makarantar ta fitar da sanarwa.

Tiktoker: Kira na karuwa da malamin makarantar yayi ya ɓatamin rai sosai - Rahama Sa'idu
Tiktoker: Kira na karuwa da malamin makarantar yayi ya ɓatamin rai sosai – Rahama Sa’idu

Amma idan zaku tuna mun kawo muku labarin wani dan jarida Ahmad Nagudu inda yake karya ta labarin da wannan yarinyar ta fadi inda yace daman yar duniya ce domin asalinta iyayenta yarbawa ne yan jihar oyo, asalin ramatu amma ta chanza suna zuwa rahama wanda ya kawo dalili sosai da zaka iya karanta a nan.

Gidan rediyo Freedom Radio kano sun samu zantawa da rahama Sa’idu wanda labarin korar ta daga makaranta ya kare shafukan sada zumunta ga yadda tattaunawar su ta kasance.

“Akwai wani malami bansan miye tsakanina da malamin ba a wani lokaci yana iya kirana yayi ta zagina, haka kuma wani ya kirani a ofis dinsa yake ta zagina ya. Kirani karuwa banza karuwar wufi akan wannan wakar ta sanata Adamu aleiro ina nan ina talla kaina, amma kawai hakuri na bashi saboda suna gabana kuma makarantar su ce.

Kirana karuwa wannan kalma ya ɓata min rai Sosai na so na kai shi ƙara amma ina fitowa a ofish din nashi sai na kira yayan mahaifina da kuma babana nayi musu bayanin abinda ya faru sukace kawai nayi hakuri shikenan me zance.

Akwai lokacin da har ya tashi hanani jarabawa ba kawai dai malamin baya sona ne, kuma maganar gaskiya babu abinda ya hadani da shi -inji rahama

Yadda na dauki karatu na da muhimmanci idan zamu rubuta jarabawa wani lokacin nakan sai da wayata, idan ma ba’a samu sayar da wayar ba nakan bada ajiyar wayana sai na gama jarabawa sai na karba” – inji rahama.

Miye alakari tiktok da korar ki da ankayi ?

 

Abinda yasa nace tiktok ne saboda a gaskiya ban taba tunanin malami zai iya shiga rayuwar dalibi ta daban bana tunanin haka kuma baya cikin dokar makaranta

Baki ganin a makaranta ba ilimi kawai ake badawa a makaranta ba saboda malamai sun dauki dalibai kamar ‘ya’yansu ?

 

Eh to hakane amma ni ai inda yana hanani karatu na ne, kuma idan har yana hanani karatu ba wai kora ta za’a yi ba, ya kamata a kirani gashi kuma ni gaskiya bai taɓa hanani karatu na ba gaskiya

Zaku iya sauraren cikakken firar da shi Gidan jaridar Freedom Radio kano sunkayi da ita rahama Sa’idu domin wannan bayyani da munka rubuta muku mun tsakure ne kadan daga cikin abinda ta fada.

Ga bidiyon nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button