Tauraruwar wasan Tennis ta sadaukar da dukiyar ta ga Falasdinawa
“Yana da matukar wahala ganin yara, jarirai suna mutuwa kowace rana,” in ji Jabeur, tana mai share hawaye yayin da take magana game da yakin Isra’ila da Gaza bayan nasarar da ta samu a gasar WTA a Mexico.
Tauraruwar Tennis ‘yar kasar Tunusiya Ons Jabeur ta ce za ta bayar da gudummawar wani bangare na kyautar da ta samu daga wasan karshe na gasar kwallon tennis ta mata (WTA) ga Falasdinawa da ke fuskantar kisan kiyashi daga sojojin Isra’ila a Gaza.
Jabeur wacce ke share hawaye tsabar takaicin abinda ake wa Falasdinawa a yayin da take magana da manema labarai jim kadan bayan nasarar da ta samu kan Marketa Vondrousova a Cancun ranar Laraba, kamar yadda majiyarmu ta wakiliya na ruwaito
“Na yi matukar farin ciki da nasarar, amma bana farin ciki kwanan nan,” in ji Jabeur lokacin da aka tambayar ta
Wakiliya ta ruwaito Jabeur na cewa, “Halin da duniya ke ciki musamman a Gaza yana damu na, …ta dakata da jawabi sannan ta yi ajiyar zuciya daga nan ta gaggauta sauka daga kan microphone ta rushe da kuka.
“Yana da matukar takaici ganin yadda yara, jarirai suke mutuwa kowace rana,” in ji ta.
“Abin takaici ne, don haka na yanke shawarar bayar da gudummawar wani bangare na kyautar kyautar don taimakawa Falasdinawa.”
‘Ina son zaman lafiya a duniyar nan’
Matashiyar mai shekaru 29 ta sha yin magana kan batutuwan da suka shafi rikice-rikice, musamman a yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.