Rarara yayi Gaskiya: Tabbas akwai bukatar Buhari ya nemi gafarar ‘yan Nijeriya – Gudaji Kazaure
Tsohon dan majalisar tarayya hon.Gudaji kazaure ya to fa albarkacin bakinsa akan wannan dambar da rarara yayi inda an dade ba’a ji firarsa ba, da manema labarai ba.
Hon. Gudaji Kazaure tsohon dan majalisar tarayya yana daya da cikin yan siyasa da wannan jaridar ta Dclhausa ke gayyato wa a wannan lokacin abinda ya fahimta da ke tafiya shine akan firara rarara da yan jaridar yayi kura kurai guduma biyu kuma yayi gaskiya waje daya.
Hon.Kazaure ya tabbatar da maganar rarara akan cewa tabbas akwai bukatar buhari ya nemi ya fiyar yan najeriya, amma kuma ya musanta cewa maganar kwana dari na wannan gwamnati yafi na shekara 8 din Buhari wannan zancen gata ce babu gwamnatin da talaka ya samu a najeriya irin gwamnatin Muhammadu Buhari ga abinda yake cewa.
” Yace duk najeriya babu wanda yake ji wajen bada gudunmawa buhari yaci sai mutum daya shine bola tinubu sai shi wannan kuskure ne sosai ya tafka na farko, domin idan ka kalli App, ANpp ,cpc har zuwa Apc 2015 shine tubalin da anka gina har buhari yaci zaɓe
Kuma ina ganin ni kaina hon.kazaure nafi rarara bada gudunmawa ga cin nasarar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin a shekarar 2014 na dauki tawagar malamai nakai su kasar Saudiyya domin suyi addu’a Allah ya baiwa buhari nasara akan zaben da zai tsayawa a gaba yaba ya zabi zabuka da yayi a baya.”
“Anyi sakaci mai girma daga ɓangaren mai girma Muhammadu Buhari wanda ya bari anka ajiye shi wasu “local champion” sunka aje shi a cikin fadar shugaban kasa villa sunka ringa yimai wayo, wanda duk anka wahala da su ankayi bata bata anka ture su.
Yayi sakaci anka hada shi da wasu fada anka rabashi da masoyansa na asali wandanda zasu iya bada jininsu wajen fito da mutuncin shi, anka kawo baki wasu bai taba ganinsu ba, anka basu ministoci da manyan wurare sunka dinga azurta kansu wanda su da gangan sunka bar masa irin wannan bakin jini da rarara yace cewa ya lalata gwamnati.
An cire makudan kuɗi an kauce da su da sunan shi wannan babban saka ci ne da yayi na yarda da rarara a nan”- inji hon.kazaure.
“Amma magarsa ta cewa kwana darin wannan gwamnati yafi na shekara takwas 8 din mai girma muhammadu buhari wannan ina da ja, a gurguje zan iya sanar da kai lamarin boko haram yayi maganinsa, tituna babu shugaban kasa da yayi tituna kamar sa kudu da arewa mutane ne basu sani ba, idan kaje aikin N-power ba’a taba gwamnatin da ta damkawa talaka kuɗi ba wuri na guri a bashi ta hanunsa ko ta akawun dinsa da mai girma muhammadu buhari yayi rabo ba.
Ga bidiyon nan ku saurari sauran bayyanai sosai a ciki.