Labarai

Mrbeast yasa an binne shi da ransa saboda neman kuɗi da “followers” sati Daya

Advertisment

Wani labari mai ban al’ajabi wanda tabbas akwai isgili da sakaci da rayuwa kawai dan neman abin duniya da mabiya “followers” har na ka sanya a binne ka har na tsawon mako daya.

Mrbeast mutum ne da yafi kowa mabiya “followers” a shafin YouTube wanda yanzu haka yana da mabiya a shafinsa na YouTube ‘channel’ da ya kai miliyan dari biyu da sha ukku 213.

Mrbeast mutum ne da yayi wannan abu da duk duniya ba’a taba ji ko gani ba, mrbeast dai burinsa ya cika domin kuwa yanzu kwana biyu dora wannan labari har ya samu wandanda sunka kalle shi sama da mutum miliyan sittin da hudu 64.

Mrbeast ya sanya an haƙa an sanya shi a ciki, abinda mai karatu zai fara tunani ko tambaya shin yana raye ko shiga da abinci, ruwa da dai sauransu, tun kafin ya shiga wannan rame sai da ya sanya anka haka masa kamarori da za’a iya ganin duk motsinsa da kuma jinsa ta harya shiga da wayar tarho da yana magana domin idan yana neman a kawo masa dauki.

Advertisment

Mutane da daman sun nuna wannan rigan liman masallaci ne domin bai kamata baka mutu ba kana yiwa matata isgili ba, wasu kuma na ganin hakan zai iya zamo izina da darasi akan yadda zaman kabari yake idan ya bada labari duk da yake bai mutu ba, ya shiga da abinci, ruwa da abubuwan more rayuwa.

Mrbeast bayan ya cika kwana bakwai 7 mako daya kenan ya nemi a fitar da shi domin bazai iya rayuwa a cikin wannan kabari ba, a lokacin da anka fara fitar da shi ganin hasken rana kawai yayi murmushi da murna na fitowarsa, inda mutane sun zo wajen domin yaba masa irin wannan abun al’ajabi da yayi kuma burinsa ya cika yazamo mutum mafi yawan mabiya “followers” a kafar YouTube.

Ga bidiyon nan kasa…

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button