Kannywood

Martani zuwa ga Abdallah Amdaz daga furodusa alhaji shehe

Daya daga cikin furodusa masana’atar kannywood mutsapha ahmad alhaji shehe ya tura wani sako zuwa ga dan uwar sana’arsa Abdallah Amdaz wanda yayi jawabi a hukumar hisbah da ya jawo cece kuce.

Alhaji sheshe ya fitar da wannan sakon ne a shafinsa na sada zumunta inda ya wallafa kamar haka.

Ni Mustapha ahmad alhaji shehe ina kira ga abdallah amdaz daya gaggauta fitowa duniya ya zaiyanawa duniya sunayen wadanda suke aikata laifukan daya lissafawa hukumar hisbah ta jihar kano.

Idan kuma ba tabbas ni zan dauki matakin Shari’a dan ganin na tabbatarwa iyaye na da makusanta na, bana daya daga cikin waɗanda yake nufi a Masana’atar Kannywood da kalmomin sa, marasa daraja a cikin addinin mu da kuma al’adar mu.”inji alhaji sheshe.

Hausaloaded ta samu tattaro martanin mutane kamar haka

 

@sani candy cewa yake:

Magana ta gaskiya kenan wllh bazan yafewa amdaz ba.

@Alhajin Allah cewa yake :

Idan kasan baka daya daga ciki karabu dashi, Allah zai bayyana gsky.

@jamilu kaida cewa yake:

Gaskiya ni banga aibu a maganarsa ba, shi bai kama sunan kowa ba, riga ce ya dinka ba wuya, kuma kayi karansa kace yace maka me? Kuma wallahi Majorityn mutane sungamsu gaskiya ya fada, kai meye naka in har baka daga cikin wadanda yake ganin suna da matsala. A shawarce kana da kima da mutunchi a idon mutane kar ka yarda ka barar da kimarka akan wani abu marar dalili, gaskiya daya ce daga qinta.

@tittlehabeeb cewa yake yi:

Toh Kai meyasa abin ya dameka tunda kasan baka cikin wadan da suke ciki? In kayi haka kayi yarinta wallahi. Dayawa nasan suna ganin darajarka Kuma tunanin su bazai taba kaiwa kan irinku ba, kaima kasan da wadan da yake duniya ma tasani. Yunkurin yin wannan abun dakace zakayi in har kayi to yarinta ce zalla.

@itz_official_ bash856 yana mai cewa :

Gaskiya wannan ba daidaibane Amma a fahimtata saboda abubuwan da yayi mentioned idan harba mutum ba aikatasu yake wlh wannan abun baxai dameshi, saboda hk amatsayina na masoyinka ina baka shawara kabar wannan maganar please.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button