Kannywood

Mansurah Isah ta buƙaci iyaye da su kai ƴaƴansu mata ayi musu allurar rigakafin HPV

Shahararriyar Jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta bukaci iyaye da su kai ƴaƴansu mata a yi musu allurar rigakafin cutar sankarar mahaifa, wacce a turance ake kira da Human Papillomavirus, HPV, Vaccine, domin kare su da ga kamuwa da cutar sankara da sauran nau’o’in kansa.

Jarumar ‘, haifaffiyar jihar Kano, marubuciya kuma mai shirya finafinai ta yi wannan kiran ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa a jiya Lahadi, a Abuja.

Majiyarmu ta samu daga Daily Nigerian Hausa,Mansurah ta ce kwanan nan ta dauki ‘yarta ɗaya tilo ta kai ta a yi mata rigakafin cutar ta HPV, inda ta kara da cewa, wannan shi ne karon farko da ake ba da irin wannan rigakafin kyauta.

A cewarta, a shekarun baya, allurar rigakafin ta kai Naira dubu 40,000 zuwa Naira dubu 60,000.

“Don haka ina so in yi amfani da wannan dama a matsayina na ’yar fim, ’yar kasuwa, mai bayar da agaji da kuma taimakon jama’a domin jan hankalin mutane su sani cewa rigakafin cutar ta HPV kyauta ne kuma ya kamata ‘yan matanmu, iyayen mu mata da su je a yi musu

“Dalilin da ya sa ya ke da muhimmanci a yi allurar shi ne don a taimaka wajen rigakafin cutar kansar mahaifa wanda a kasar Hausa muke kira da ‘Cutar Sankarar Mahaifa’, inji ta.

Ta kara da cewa cutar sankarar mahaifa gaske ce don kwanan nan ma kakar kawar ta aka gano ta kamu da cutar, inda ta jaddada cewa gaske ce cutar ba ƙarya ba ce







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button