Labarai

Kotu ta raba auren shekara 10 bisa matsawar mahaifin matar na arabu kan za ai wa ƴarsa kishiya

Kotun Shari’ar Muslunci da ke zaman ta a hukumar Hisbah ta jihar Kano ta datse igiyar auren wasu ma’aurata bayan sun shafe shekaru 10 tare.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tun da fari ne matar, Amina Muhammad, ta kai ƙarar mijin nata, Aliyu Abdurraham Aliyu, inda take neman a raba auren su saboda bata don a yi mata kishiya.

Kotu ta raba auren shekara 10 bisa matsawar mahaifin matar na arabu kan za ai wa ƴarsa kishiya
Kotu ta raba auren shekara 10 bisa matsawar mahaifin matar na arabu kan za ai wa ƴarsa kishiya

Wannan jaridar ta kuma rawaito cewa ana zargin mahaifin matar, wanda Hakimi ne a wata ƙaramar hukuma a Kano, shi ya matsa sai an raba auren bisa hujjar cewa su gidansu na sarauta, ba a yi wa ƴaƴansu kishiya.

Saidai a zaman Kotun na jiya Litinin, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Sani Tanimu Sani Hausawa ya datse igiyar auren bayan ya karbi rokon lauyan Amina, Barista Ibrahim Umar Musa tunda an kasa samun daidaito a tsakaninsu.

A hukuncin ‘, Mai sharia Sani Tanimu Sani Hausawa ya nemi wacce tayi Kara data biya kudin Kul’i naira dubu 20 ‘, amma shi wanda a ka yi kara yana da damar daukaka kara zuwa Kotun gaba.

A zaman Kotun na farko, Lauyan wanda aka yi kara, Umar Yusuf Khalid ya bayyana damuwarsa kan yadda aka kasa samun daidaito, inda ya yi nuni da cewa sabani a zaman aure ba bakon abu bane.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a zaman kotun na baya, alkalin kotun ya umarci mijin da ya yi bikin matar sa, inda lauyan ta ya nemi ya tafi da kaji, kuma hakan aka yi, amma ko da ya je, sai aka ki bashi matar, har sai da ta kai ga kotu ta datse igiyar auren.

Abin jira a gani shi ne ko mijin, Aliyu zai daukaka kara domin ganin ya karvi ƴaƴansu 4 da suka haifa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button