Labarai

Kasafin kuɗin 2024 : Talauci,yunwa, rashin tsaro lallai su san inda dare ya yi musu gamu nan zuwa – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na farko ga ƴan Majalisar dokokin Najeriya.

Bisa ga kasafin da shugaba Tinubu ya gabatar za a kashe kudi har naira tirliyan 27.5 a 2024.

Kasafin zai mayar da hankali wajen tabbatar da tsaron kasa, samar da aikin yi, bunƙasa harkokin zuba jari da rage tsananin talauci da fatara a tsakanin al’ummar kasa.

Shugaba Tinubu ya ce an tsara kasafin kudin ne bisa hasashen sayar da gangar man fetur daya a kan dala 77.96, da hako kiyasin ganga miliyan 1.78 ta man fetur a kullum. Sannan da dalar Amurka daya a kan canjin naira 750.

Za a kashe naira tirliyan 9.92 a bangaren ayyukan yau da kullum. Sai kuma naira tirliyan 8.25 wajen biyan basukan da ake bin kasa yayin da za a kashe naira tiriliyan 8.7 wajen gudanar da manyan ayyuka.

Kasafin kuɗin 2024 : Talauci,yunwa, rashin tsaro lallai su san inda dare ya yi musu gamu nan zuwa - Tinubu
Kasafin kuɗin 2024 : Talauci,yunwa, rashin tsaro lallai su san inda dare ya yi musu gamu nan zuwa – Tinubu

Sannan kuma shugaba Tinubu ya bayyana wasu mahimman ɓangarori da gwamnati za ta maida hankali a kai a cikin kasafin kuɗin na 2024 da suka hada da:

1 – Sassauta hauhawar farashi zuwa kashi 21.4% (a yanzu alkaluman hauhawar farashi sun kai kashi 27.33

2 – Bunkasar tattalin arziki da mafi karanci kashi 3.76.

3 – Jaddada kawance tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa ta hanyar bullo da tanade-tanaden da kamfanoni za su iya cin gajiyar aiwatar da manyan ayyuka a bangaren samar da makamashi da sufuri da sauransu.

3 – Ranto kudi jimillar naira tirliyan 7.83 don cike gibin kasadin kudin 2024

4 – An yi hasashen cewa gibin kasafin kudi a kan naira tirliyan 9.18 a 2024

5 – Hasashen biyan basuka da kashi 45 na jimillar kudin shiga da Najeriya ke sa ran samu.

6 – Bunkasa rayuwar ƴan Najeriya da ba da fifiko ga kananan yara a matsayinsu na ginshikin al’umma.

6 – Magance tsoffin matsalolin da aka dade ana fama da su a bangaren ilmi, ta hanyar aiwatar da karin tsari don samar da kudi ga ilmi mai zurfi, ciki har da shirin bashin karatu ga dalibai wanda zai fara aiki daga watan Janairun 2024.

Hakazalika

Bayan Gabatar da Kasafin Kudi, Tinubu Ya Hilla Kasar Waje

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tashi daga birnin Abuja na Najeriya zuwa birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa

Shugaban Zai bi sahun sauran shugabannin Kasashen duniya don tattauna muhimman Bayanai

Tinubu Zai Samu rakiyar manyan jami’ian Gwamnatin sa

A yayin taron da aka shirya gudanarwa a ranakun 1 da 2 ga watan Disamba, 2023, Tinubu zai gabatar da jawabi da zai bayyana matsayin Najeriya kan batutuwa daban-daban da suka hada da makamashi mai sabuntawa da kuma samar da kudaden yanayi.

Wata sanarwa da mai baiwa Tinubu shawara ta musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Talata ta ce shugaban zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnati.

Mun ta rawaito cewa shugaban kasar ya bar kasar ne sa’o’i kadan bayan gabatar da kasafin kudin shekara ta 2024 ga taron hadin gwiwa na majalisun dokokin kasar.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button