google-site-verification=WmtThtgKMuimwQoXo8Cd4z9ZhII1jY-1XVfjGSvL5r8
Labarai

Kano: Zamu tsaftace amfani da Tiktok, ƴan titkok sun jaddada wa hisbah

Ƴan TikTok a jihar Kano sun tabbatar wa da Hukumar Hisbah cewa za su tsaftace amfani da TikTok da zai yi daidai da koyarwar addinin Musulunci da al’adar Hausa.

Ƴan TikTok din, su sama da 200, sun bayyana hakan ne yayin da su ka amsa kiran da Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa ya yi musu a yau Litinin, domin yi musu nasiha, a wani ɓangare na “Operation Kau da Baɗala” da Hisbah ke yi a fadin jihar.

Wasu daga cikin yan TikTok din sun nuna jin dadinsu game da taron da suka yi tsakaninsu da Hukumar, inda su ka yi alkawarin canza akalar abubuwan da suke yi wanda suka saba sharia.

Kano: Zamu tsaftace amfani da Tiktok, ƴan titkok sun jaddada wa hisbah
Kano: Zamu tsaftace amfani da Tiktok, ƴan titkok sun jaddada wa hisbah

Khadija mai bakin kitse ta bayyana cewa ta amfana da zaman da ta yi da Hukumar ta Hisbah inda ta ce daga yanzu ta daina sanya raye -rayen banza a shafukanta.

“Gaskiya na ji dadin wannan zama da muka yi Kuma insha Allah daga yanzu na daina sanya rawa a shafina. Zan canza zuwa abubuwa na alheri. Ina Kiran sauran yan uwana yan TikTok da suka tsorata suka ki zuwa da su yi kokari su halarci zama na gaba”

Shi ma wani mai suna Alamin da aka fi sani da Na Annabi ya ce a yanzu ya shirya tsaf wajen ganin ya yi watsi da abubuwan da yake yi don ci gaba da karatunsu.

Daily Nigerian Hausa na ruwaito.Fiye da yan TikTok 200 ne suka halarci taron wanda kuuma Hukumar Hisbah ta gwangwaje kowannensu da Naira dubu biyu a matsayin kudin mota.

A nasa bangaren, Sheikh Daurawa ya ce hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa za ta hada kai da yan TikTok din wajen gyara abubuwan da su ke yadawa a shafukansu don amfanin alumma.

Tunda fari, Shaikh Daurawa ya ce sun kira taron ne don a tsaftace harkar TikTok a tsakanin matasan jiha a wani mataki na operation kawar da badala.

“Mu dama Hisbah aikinmu shi ne umarnin da aikin alheri da kuma gani da mummuna. Idan an duba kwanan nan mun himmatu wajen kawar da badala a wannan jihar hakan ya sa muka ga dacewar zama da yan TikTok don mu ga sun tsaftace ayyukan da suke yi a maimakon yada abubuwan badala da suke su koma su rika yin amfani da shafukansu wajen yada ayyukan alheri”

Hukumar ta kara da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta tanadi wu tagomashi ga matasan don ganin sun amfana.

“Mai girma Gwamna ya tanadi abubuwa hudu ga yan TikTok din za a aurar da masu son aure a cikinsu, Masu son sanaa za a ba su jari. Haka su ma masu son karatu za a dauki nauyin karatunsu daga nan har zuwa Landan. Su ma wadanda ke da marsaloli na damuwa ko rashin lafiya za a sama musu magani tare da ba su shawarwarin da za su canza tunaninsu”

Shaikh Daurawa ya bayyana cewa daga
yanzu Hukumar za ta bude shafi na musamman tare da yn TikTok din don tattaunawa tare da bibiyar abubuwan da suke yi a shafukansu don sanin ko sun canza halayyarsu ko kuma a’a.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button