Kalaman ɓatanci ga Buhari da gwamnatin sa: An maka Rarara a kotu
Wani mazaunin garin Maraba da ke jihar Nasarawa, Muhammed Sani Zangina, ya shigar da kara kotu, inda ya zargi mawakin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu, wanda ake kira da Rarara, da tada hankalin jama’a.
A tuna cewa Rarara, a yayin wani taron manema labarai kwanan nan a Kano, ya bayyana nadamar goyon bayan tsohon shugaban kasar, wanda ya zarge shi da lalata kasar kafin mikawa shugaba Bola Tinubu mulki.
Daily Nigerian Hausa na ruwaito A wata takardar ƙarar da kotu ta bayar ga City & Crime, wanda ya shigar da karar, ta hannun lauyansa, Muhammed Barde Abdullahi, ya ce matakin na Rarara na iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a, da kuma kawo hargitsi, wanda ya saba wa sashe na 114 na kundin laifuffuka.
Sai dai kuma ba a yi zaman sauraron ƙarar, wacce aka shigar a wata kotun majistare dake zamanta a jihar Nasarawa ba a jiya Litinin 13 ga watan Nuwamba, saboda rashin halartar wanda ake kara.
Mai gabatar da kara na kotun ya bayyana cewa ba za a iya aika sammacin da kotun ta yi wa wanda ake tuhuma ba.
Daga nan sai Barista Abdullahi, ya nemi a canja hanyar baiwa wanda ake kara sammaci, inda kotun ta amince.
Alkaliyar kotun, Maryam Nadabo, ta dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Disamba.