Kannywood

Idan Na samu Jarin yin sana’a zan daina fim gaba ɗaya – Abdallah amdaz

Idan Na Samu Jarin Yin Sana’a Zan Daina Yin Harkar Fim Gaba Ɗaya, Céwar Jarumin Da Ya Tona Asirin Ƴan Fim Abdullahi Amdaz

Tattaunawar Jarumin Kannywood Abdullahi Amdaz da wani fitaccen mai amfani kafar sada zumunta da ya wallafa a manhajar facebook Bukhari Mu’azu Abubakar

Sunana Abdullah Amdaz Wanda aka fi sani da Excellency Kuma dalibin ilmin addinin musulunci ne nayi karatu a sudan, Kuma mahaddacin Alqur’ani ne da Allah ya jarabceni da shiga harkan film saboda Wasu dalilai.

Idan Na samu Jarin yin sana'a zan daina fim gaba ɗaya - Abdallah amdaz
Idan Na samu Jarin yin sana’a zan daina fim gaba ɗaya – Abdallah amdaz

Kadan daga ciki shine narasa jarina na kasuwa wanda abaya ina saida yaduka da shaddodi, nayi kokarin a taimakeni don naga ban fada a wancan harka ba abun ya ci tura, Na rantse da Allah nakan yi kwana 3 ban samu abinda zan kai gida ba.

Wanda haka ne ya tilasta min shiga harkar film ta hannun Musa mai sana’a ya taimake ni a lokacin da nake bukatar taimakon.

yanzu Haka a masana’antar suna yimin barazanar cewa ko na janye maganar da nayi na basu hakuri ko su dakatar dani daga harkar.

Alhmdulilah ya tabbatar mun da cewa Wallahi idan Yasamu jari mai kyau zaibar harkan nan Kuma yayi mun rantsuwa da Allah cewa ko yau saida Ya roki Allah acikin sallah da asuba akan ubangiji ya canza masa da sana’ar da tafi wannnan. Kalubale ga mutane Masu mutunci da Addini. Wallhi idan da munada kishi da zuciya zamu iya hadawa wannnan Bawan Allah jari mai suna jari yacigaba da kasuwancin sa Tare da Da’awa wa musulunci.

In sha Allah zamu hadu dashi nan kusa Yabamu time venue don muga mun Bashi gudumawar data dace.

Yan’uwana muyi sharing Tare da Masa addu’a da fatar alkhairi ubangiji Yasa yadaina wannnan harkan.

Bukhari Muazu ya sake wallafa wani rubutun inda yake cewa.

KAMAR BAKU FAHIMCI SAKON DAI DAI BA…

Wannnan Bawan Allah danayi Magana dashi wallhi Bai bukaci cewa sai anbashi jari ko sai antaimakeshi kafin Yabar sana’ar film ba, nine nake ganin dacewan mutaimaka masa don karfafashi domin abokanan sana’ar nasa Yanzu zasu zama abokan fadar sane. Inaga Abunda Yafi kamata mu maida hankali shine shin dagaske idan Yabar sana’ar film akwai gudumawar da zai bayar ta fuskan Addini? Idan akwai to wajine muyi iya kokarinmu wajen ganin mutsaya Tare dashi don cikan burinsa. Allah Yasa mufahimci sakon da budaddiyar zuciya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button