Kannywood

Hadaka kungiyar mawaka sun nesanta kansu da kalaman Rarara ga Buhari

Advertisment

Kungiyar murya daya ta mawaka inda sunka nesan ta kansu da cewa basa tare da kalaman da dauda kahutu rarara wanda ya caccaki tsohon shugaban kasa muhammadu buhari da kuma suka ta yadda ya gudanar da mulkinsa.

Shugaban kungiyar murya daya wato mawaki Ali isah jita yace sun tara wannan taro ne na manema labarai domin su nisantar da kansu dangane da kalaman rarara yayi inda ya ce Dauda kahutu rarara yayi wadancan kalamai ne a bisa ra’ayin kansa.
Amma fa ba tare da wayun mawaka ba.

Hadaka kungiyar mawaka sun nesanta kansu da kalaman Rarara ga Buhari
Hadaka kungiyar mawaka sun nesanta kansu da kalaman Rarara ga Buhari

“Kungiyar murya daya ta nazarci duk kalamai da yayi wanda sunka haddasa cece kuce musamman a kafaffen yada labarai da kuma dandalin sada zumunta na arewacin kasar nan biyo bayan abubuwa da sunka gudana, hakan ya wajaba mu fito domin nisantar da kan mu da al’umma musamman kamar abubuwa kamar haka:-
Na daya kalamansa ba kalamai ne da sunka wakilci dukkan mawakan arewacin najeriya ba, wala Allah ɗai ɗai kun mu ko kungiyan ce ba. Ba adalci bane a auna dukkan bisa doran kalaman nasa sunka ƙunsa ba, al’umma sun sani yayi kalaman ne a madadin kansa da kila yaran ofishin sa.

Mu kungiyar murya daya bama goyon bayan kalaman sa da dalilai masu dama wanda zaku saurara daga mai magana da yawun kungiyar kuma kuma ma’ajin wannan ƙungiya Wato alhaji el-muaz Ibrahim birnewa” – inji Ali jita

“Muna kara jaddadawa da babba murya bama tare da abokin sana’ar mu yayi saboda dalili kamar haka

Dalili na farko mu a matsayin na kungiya bamu amince da kowane tozartawa da wani dattijo da ke arewacin najeriya ba, ba daidai bane a dinga yiwa mawallafa kudin goro saboda aikin mutum daya tal a cikinsu wanda har a wayi gari wasu kalamai na iya biyo bayan marasa kyau ga wasu mawallafan da abun bai shafe su ba.

Kungiyar murya daya ta azawa kanta nauyin kare martaba duk wani mutum mai mutuncin a arewacin najeriya bisa tsohon shugaba da wanda yake kan karagal mulki , ba tare da la’akari da siyasa ko ƙabilanci ba, kuma idan wani yafi yace gudumuwarsa tafi ta kowa to kila fahimtar sa ce.

Mu munsa minene waka da tasirin ta kuma munsa irin gudunmawar da waka ke iya bayarwa a siyasance a cikin al’umma kamar yadda malamai kan fito suyi kira da wa’azi ga alumma da a zabi shugaban da ya dace malamai suna taka rawar gani fastoci sunayi , iyaye suna tasu rawar gani ga ‘yayansu da magabata suna yi ga na ƙasa da su masu tasowa suna bada gudunmawa dan a zabi shugaba.

Bai dace wani ya fito yace iya gudumuwar da waka take bayarwa tafi ta kowa a siyasance – inji el-muaz

Ga cikakkiyar firar nan domin ku saurara kuji daga bakin shuwagabanni kungiyar.

Ga bidiyon nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button