Labarai

Gwamnatin Jihar Katsina za ta cigaba da yin haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da ingantaccen tsaro a jihar Katsina – Dr. Nasiru Mu’azu Ɗanmusa

Ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar Katsina (Ministry Of Internal Security And Home Affairs) ta jaddada ƙudurinta na inganta Hulɗar aiki da dukkanin hukumomin tsaro na jihar.

Kamar Yadda Kwamishinan tsaro na cikin gida Dr. Nasiru Mu’azu Danmusa ya bada wannan tabbacin lokacin da ya Ziyarci kwanturolan hukumar kwastam na Jihar Katsina.

Dokta Nasiru Mu’azu ya Bayyana Cewa Ma’aikatar ta samu nasarori da dama dangane da kalubalen tsaro wanda shine babban Maƙasudin kafa ta.

Gwamnatin Jihar Katsina za ta cigaba da yin haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da ingantaccen tsaro a jihar Katsina - Dr. Nasiru Mu'azu Ɗanmusa
Gwamnatin Jihar Katsina za ta cigaba da yin haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da ingantaccen tsaro a jihar Katsina – Dr. Nasiru Mu’azu Ɗanmusa

Kwamishinan ya danganta nasarorin da aka samu basa rasa Nasaba da jajircewar Gwamna Dikko Umar Radda da kuma goyon baya da haɗin kai da hukumomin tsaro ke bayarwa.

A nasa jawabin, Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Jihar Katsina, Mista M.A Umar, ya ce Hukumar Kwastam da ke karkashin sa na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da tsaron duk wani kaya da ake jigilarsu a cikin Jihar kamar yadda doka ta tanadar, shafin katsina reporters na ruwaito daga mataimaki na musamman akan al’amuran gida da tsaro a cikin jihar falalu lawal katsina

Sana Ya ba da tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba da aiki tare da ma’aikatar tsaron cikin gida saboda mahimmancin ma’aikatar.

Kwamishinan ya samu rakiyar babban sakataren ma’aikatar Barista Nasiru Almu da kuma shugaban ƙaramar hukumar Batsari da Magajin Garin Batsari.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar tsaron cikin gida Tukur Hassan Dan-Ali ya sanyawa hannu.

 Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button