Gwamnan Kano ya bada umarnin kwashe masu taɓin-hankali a kan tituna zuwa aisbiti
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin kwashe illahirin masu larurar ƙwaƙwalwa da ke gararamba a kan titunan jihar a birni da ƙauye.
Fauziyya D Sulaiman, hadima ta musamman ga Gwamnan kan harkokin jin-ƙai ce ta shaida hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na facebook a yau Talata.
Ta ce gwamnan ya bada umarnin ne bayan koke-koken da al’umma su ka shigar ga gwamman.
Ta kara da cewa tuni dai aka fara aikin kwashe masu larurar zuwa asibitlcin masu larurar ƙwaƙwalwa domin kulawa da lafiyar su.
“Bayan koke-koke da aka shigar gurin mai girma Gwabnan Kano H.E Abba Kabir Yusuf akan masu larurar kwakwalwa da ke yawo akan titunan Kano cikin birni da kauye wasunsu ma tsirara suke yawo, wasu ana cutar da rayuwarsu musamman mata, kuma ba su da galihun da zaa dauke su akai su asibiti, mai girma Gwabna ya bayar da umarnin a kwashesu akai su Asibitin masu Larurar kwakwalwa domin kulawa da lafiyarsu.
“Yau muka fara wannan aikin karkashin hukumar Agajin gaggawa (SEMA) da kuma office dina, SSA Needy and Valnurble,” in ji ta.