Labarai

Gaggan da suka maida garkuwa hanyar samun kuɗi ne ba su son a kawo ƙarshen ‘yan bindiga – Matawalle

Advertisment

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya ɗora alhakin kasa magance matsalar tsaro a Arewa maso Yamma kan wasu mutanen da suka maida harkar garkuwa da mutane hanyar samun kuɗi.

Matawalle ya yi wannan iƙirarin ne a tattaunawar sa da Kamfani Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a Abuja.

“Akwai harkar samun kuɗi a ta’addancin ‘yan, kuma masu samun kuɗi a harkar ke ƙara ruruta fitinar a ƙasar nan.

Gaggan da suka maida garkuwa hanyar samun kuɗi ne ba su son a kawo ƙarshen ‘yan bindiga – Matawalle
Gaggan da suka maida garkuwa hanyar samun kuɗi ne ba su son a kawo ƙarshen ‘yan bindiga – Matawalle

“Gungu-gungun waɗanda suka maida harkar garkuwa da ta’addanci ne ba su son a kakkaɓe ta’addanci a ƙasar nan. Mutane da yawa a Arewa na da hannu a harkar garkuwa da mutane.

Advertisment

“Na kira abin ‘biznes’ saboda masu sayar wa ‘yan bindiga muggan ƙwayoyi ba su so a kawar da matsalar tsaro, masu sayar masu da abinci da fetur da sauran kayan masarufi duk ba su so a ga ƙarshen wannan fitinar.

“Sai kuma mutane a cikin gari masu yi masu leƙen asiri, su na gulmata masu wanda za a kama a samu kuɗi. Su ma ba su so a kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro. Saboda ‘yan bindiga su na biyan su ladar ganin-ido, don haka ba su so a daƙile masu hanyoyin samun kuɗi.

“Saboda haka ba su so wannan mummunan al’amari ya kawo ƙarshe, da yawan mutane sun haɗa kai da ‘yan bindiga su na samun tulin kuɗaɗe.” Inji Matawalle.

Ministan wanda shi ne Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya gaji kujerar gwwmna a zaɓen 2023 a Zamfara, ya ce a lokacin da ake sayar da kwalbar Coca Cola Naira 100 a cikin garuruwa, sai aka samu wasu marasa kishi na kai wa ‘yan bindiga Coca Cola har cikin daji, su na sayar masu N500.

“Kuma lokacin da ake sayar da buhun shinkafa Naira 18,000 ko Naira 20, to marasa kishi na kai masu har cikin daji su na sayar masu kan Naira 80,000.”

Daga nan Matawalle ya ce aikin samar da tsaro ya rataya a wuyan baki ɗayan jama’a baki ɗaya.

Daga nan ya yi kiran a ajiye wani bambance-bambance a haɗu a magance matsalar tsaro.

Ya ce ba don wasu matakai da ya ɗauka lokacin ya na gwamna ba, to da yanzu Arewa na nan a ta babbake da wuta.

“Ka tuna ni ne gwamnan farko da ya fara yanke dukkan hanyoyin sadarwa waya a jihar sa.

“Na yanke hanyar sadarwar don jami’an tsaro su samu damar kutsawa daji su ragargaje su.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button